FA da Premier sun amince asiyawa da Sir Jim Ratcliffe kashi 25 na Manchester United

..

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Hukumar Premier da ta FA ɗin Ingila sun amince a siyarwa da Sir Jim Ratcliffe kashi 25 cikin 100 na Manchester United.

Darajar kuɗin da biloniyan Burtaniyan ya sayi United ta kai dala biliyan 1.3 daidi da fan biliyan 1.03.

Iyalan Glazer ne za su zama ma su hannun jari mafi yawa a ƙungiyar sai dai kamfanin Ineos mallakin Ratccliffe ne zai ci gaba da gudanar da harkokin kwallon kafa a ƙungiyar.

Ba za a kammala cinikin ba sai bayan an kammala sa hannu kan takardun hannun jarin, wanda za a yi a daren ranar Juma'a a Amurka.

Amincewar da Premier ta yi ya ta'allaƙa ne da yadda aka kammala cinikin.

"Yanzu Premier na jiran a kammala biyan kuɗin," kamar yadda hukumar gasar ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar, yayin da a gefe guda ta tabbatar da kammala sa hannun da Ratcliffe mai shekara 71 ya yi.

Wannan ne ciniki irinsa na farko da aka gudanar ƙarƙashin amincewa Premier, wanda mambobin ƙungiyar suka amince da shi a watan Maris ɗin 2023 kuma ya ƙunshi sanya idanun wasu masu sanya idanu masu zaman kansu.

Dan kasuwar ya amince ya sayi kashi 25 cikin 100 na hannun jarin ƙungiyar, wanda iyalan Glazer ne ke da mafi yawansa, waɗanda suke da kashi 69.

Ci gaba da lura harkokin wasannin ƙungiyar na nufin kamfanin Ineos ne zai ci gaba da gudanar da harkokin kwallon maza da mata da kuma wajen koyar da kwallon yara.

Sannan za su samu kujera biyu a Manchester United PLC da kuma kwamitin amintattu a ƙungiyar kwallon ƙafa na Manchester.

Ratcliffe tuni ya ziyarci filin wasa na Old Trafford da kuma filin atisayen ƙungiyar lokacin da yake tsammanin a ƙare cinikin.

BBC ta gano cewa ana ci gaba da tattaunawa wadda take mai dadi domin kammala cinikin.

A 2005 Iyalan Glazer suka sayi Manchester United kan kuɗi fan miliyan 790.

A watan Nuwambar 2022 ne iyalan da suka fito daga Amurka suka nuna alamun sayar da ƙumgiyar domin karkata kasuwancinsu zuwa wani bangaren.