Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan fashi sun shiga gidan Aubameyang yana tsaka da bacci
'Yan fashi da makami sun shiga gidan dan kwallon Barcelona, Pierre-Emerick Aubameyang da sanyin safiyar Litinin.
Tuni 'Yan sanda suka fara binciken lamarin da ya faru a garin Castelldefels, wanda yake daf da birnin Barcelona.
El Pais ta bayar da rahoton cewar 'yan fashin sun balla kofar gidan, sannan suka shiga suka tarar da dan wasan, wanda suka yi wa barazana da shi da matarsa.
'Yan fashi da makamin sun tilastawa Aubameyang ya bude taskar da yake ajiye dukiya, inda suka sace sarkokin da ke ciki.
An kuma bayar da rahoton cewar sun lakadawa dan wasan, Barcelona duka kafin su bar gidan.
Barcelona ta fitar da jawabin cewar Aubameyang da matarsa suna cikin koshin lafiya, bayan fashi da makamin da aka yi musu.
Dan kwallon tawagar Gabon, mai shekara 33 ya yi zaman benci a wasan mako na uku a gasar La Liga da Barcelona ta doke Real Valladolid 4-0 a Camp Nou ranar Lahadi.