Mutumin da yake kara tsawo duk bayan wata uku zuwa hudu

- Marubuci, Daga Favour Nunoo
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Pidgin
- An wallafa
A shekara 2015, Sulemana Abdul Samed ya farka daga barci, amma sai wani abu ya ba shi mamaki domin ya lura cewa harshensa ya kara girma har ya cika masa baki ta yadda ba ya iya yin numfashi sosai.
Bayan ya sha magani da ya sayo a wani kemis, wanda ya rage kumburin harshen, dan makarantar babbar sakandaren bai san cewa wannan lamarin zai sauya rayuwarsa gaba daya ba.
Kuma daga wancan lokacin zuwa yanzu, Sulemana - wanda aka fi sani da sunan Awuche - ya rika kara tsawo har sai da ya kai kafa 9.6 kuma ya ci gaba da kara tsawo.
"Cikin kowane wata uku zuwa wata hudu na ke kara tsawo. Idan ba ka gan ni cikin wata uku ko hudu ba, za ka na kara tsawo," in ji Awuche yayin da yake hira da wakilin BBC Pidgin Favour Nunoo.

Tsawon da Awuche yayi ya sa ya zama wani shahararre a garinsu Gambaga yayin da mazauna garin daga kananansu har zuwa dattawan garin ke kallonsa da ta'ajibi.
"Akwai lokacin da wani dan sanda ya ce na zarce shi da tsawona, saboda haka ya ce zai dauki hoto tare da ni," kamar yadda ya tuna.
Daga 'yan siyasa zuwa ga jami'an soji da na 'yan sanda duka farin ciki da zarar sun ga Awuche, wanda baya ga cewa ya fi kowa tsawo, yana kuma da kyawun mu'amulla da sauran jama'a.
"Tsawona ya mayar da ni sahahrarre," kamar yadda ya shaida wa wakilin BBC wanda ya ziyarci garin na Awuche.
Ya kuma ce da a duk lokacin da ya halarci wani biki, sai mutane a wurin su rika matsowa kusa da shi kuma yana son haka sosai.
Ya kan kuma ba su damar daukar hoto da shi a duk lokacin da suka bukaci haka.
'Likitoci sun ce tsawona na lalura ce mai suna gigantism'

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tsawon da Awuche ya yi ba irin wanda aka saba gani ba ne, domin ko likitoci na da kiransa da sunan 'gigantism' da turancin Ingilishi.
Sun ce wannan matsala ce da kan sa mutum ya yi tsawon da ya zarce na yawancin mutane.
"Yayin da na je asibitin BMC, sai wani mutum farar fata ya ganni kuma sai ya ce inda da lalurar gigantism."
Ya kuma ce wani likitan da ya rika duba lafiyarsa ya shaida masa cewa akwai wani abu a cikin kwakwalwarsa da ya kamata a yi masa tiyata domin a cire shi.
Ya ce wannan abin ne ke sa kashinsa ke kara girma da tsawo sosai, kuma ya ce idan ba a cire wannan abin daga kwakwalwarsa ba, ba zai daina tsawo ba kuma wannan ka iya shafar lafiyarsa da ingancin walwala da jin dadin rayuwarsa.
Amma duk da haka Awuche yana fatan yin aure da haihuwar 'ya'ya, wadanda yace yake son ganin yadda za su kasance.
Kuma bai damu da cewa yafi kowa tsawo ba, domin yace haka Allah yaso ya gan shi ke nan.
"Ban damu da yadda Allah ya yi ni ba, domin ya yi ni haka ne da wani dalili nasa, wanda shi kadai ya bar wa kansa ilimin haka."
Ya kuam shaida wa BBC cewa gwaji na karshe da aka yi masa ya tabbatar cewa tsawonsa kafa 9.6 ne, sai dai BBC ba ta gwada shi ba domin tabbatar da haka.










