Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me kuke son sani kan raba jadawalin Champions League?
Kawo yanzu an samu kungiyoyi takwas da za su ci gaba da zagayen kwata fainals a Champions League da Europa da Conference League na bana.
Za kuma a raba jadawalin ci gaba da zagayen gaba ranar Juma'a, bayan da ake sa ran buga wasan karshe a filin Wembley ranar Asabar 1 ga watan Yuni.
Ba maganar fifita wata kungiya kan kwazonta, kuma kungiyoyi daga kasa daya za su iya fuskantar juna a fafatawar da za a yi gida da waje zagayen kwata fainals.
Za a raba jadawalin kwata fainals da na daf da karshe ranar Juma'a 15 ga watan Maris a Nyon a Switzerland.
Daga nan kuma za a yi jadawalin kwata fainals a Europa League da kuma Europa Conference League.
Jadawalin da za a raba zai kuma fayyace kungiyar da za ta karbi bakunci a karawar farko da kuma wadda za ta kai ziyara a fafatawa ta biyu.
Wadanne kungiyoyi ne za su buga zagayen kwata fainals a Champions League?
Arsenal (Ingila)
Atletico Madrid (Sifaniya)
Barcelona (Sifaniya)
Bayern Munich (Jamus)
Borussia Dortmund (Jamus)
Manchester City (Ingila)
Paris St-Germain (France)
Real Madrid (Sifaniya)
Wadanne kungiyoyi ne zasu kara a Europa League kwata fainals?
AC Milan (Italiya) ko Slavia Prague (Jamhuriyar Czech) (4-2)
Benfica (Portugal) ko Rangers (Scotland) (2-2)
Freiburg (Jamus) ko West Ham (Ingila) (1-0)
Marseille (France) ko Villarreal (Sifaniya) (4-0)
Qarabag (Azerbaijan) ko Bayer Leverkusen (Jamus) (2-2)
Roma (Italiya) ko Brighton (Ingila) (4-0 after first leg)
Sparta Prague (Jamhuriyar Czech) ko Liverpool (Ingila) (1-5)
Sporting Lisbon (Portugal) ko Atalanta (Italiya) (1-1)
Wadanne kungiyoyi ne a Europa Conference League kwata fainals?
Ajax (Netherlands) ko Aston Villa (Ingila) (0-0 )
Dinamo Zagreb (Croatia) ko PAOK (Girka) (2-0)
Maccabi Haifa (Israel) ko Fiorentina (Italiya) (3-4)
Molde (Norway) ko Club Bruges (Belgium) (2-1)
Olympiakos (Girka) ko Maccabi Tel Aviv (Israel) (1-4)
Servette (Switzerland) ko Viktoria Plzen (Jamhuriyar Czech) (0-0)
Sturm Graz (Austria) ko Lille (France) (0-3 after first leg)
Union St-Gilloise (Belgium) ko Fenerbahce (Turkiya) (0-3)
Wadanne ranaku za a buga wasanninn Champions League?
Za a fara wasan farko zagayen kwata fainals daga ranar 9 -10 ga watan Afirilu, yayin da za a buga wasa na biyu ranar 16-17 ga watan Afirilu.
Za a buga wasan farko zagayen daf da karshe ranar 30 ga watan Maris zuwa 1 ga watan Afirilu, sannan a yi fafatawa ta biyu ranar 7-8 ga watan Mayu a Champions League.
Yaushe za a buga kwata fainals a Europa League da Europa Conference League?
A gasar biyu za a fara wasannin farko zagayen daf da na kusa da na karshe ranar 11 ga watan Afirilu, sannan a kara a wasa na biyu mako daya tsakani.
Za a fafata a daf da karshe ranar 2 ga watan Mayu, sannan a buga wasa na biyu ranar 9 ga watan Mayu a Europa da Conference League.
Yaushe za a buga wasan karshe a Champions League?
Za a buga wasan karshe a Champions League na bana a Wembley ranar Asabar 1 ga watan Yuni.
A ina kuma yaushe ne wasan karshe a Europa League?
Za a buga karawar karshe a Europa League ta bana a filin wasa da ke Dublin a Jamhuriyar Ireland ranar Laraba 22 ga watan Mayu.
Wadda ta lashe kofin bana za ta samu gurbin shiga Champions League na 2024-25, idan ba ta samu gurbi ba a gasar kasarta.
A ina kuma yaushe ne wasan karshe a Europa Conference League ?
Za a buga fafatawar karshe a Europa Conference League na bana a filin wasa na AEK da ke Athens a Girka ranar Laraba 29 ga watan Mayu.
Duk wadda ta lashe kofin za ta fafata a Europa League na badi, idan ba ta samu gurbi ba a gasar kasarta.