Silva zai koma Real Madrid, Arsenal na zawarcin Gimenez

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid na kan gaba a jerin ƙungiyoyin da ke fatan sayen ɗan wasan Manchester City kuma ɗan Portugal mai shekara 29, Bernardo Silva (Star)
Barcelona ta shirya fafata zawarcin Bernardo Silva da abokiyar hamayyar ta, Real Madrid. are set to rival Real, domin kuwa shugaban ƙungiyar, Joan Laporta ya sha alwashin ɗauke Silva (Sport - in Spanish)
West Ham ta ƙulla yarjejeniya da ɗan wasan gaban Ingila da Manchester City mai shekara 21, Cole Palmer, amma sai Chelsea ta yi mata shigar sauri (Sun)
Atletico Madrid za ta sabinta kwangilar ɗan wasan gaban Faransa, Antoine Griezmann mai shekara 33, kuma ana sa ran kwangilar ta kai daga nan har 2026. (Rudy Galetti)
Arsenal, Juventus da kuma Atletico Madrid suna zawarcin ɗan wasan gaban Mexico, Santiago Gimenez, mai shekara 23, kuma who is ready to leave Dutch side Feyenoord. (Record - in Spanish)
Barcelona na ƙoƙarin dawo da tsohon ɗan wasan ta, Dani Olmo, mai shekara 25, daga RB Leipzig. (Mundo Deportivo) (Fabrizio Romano)
Manchester United da Arsenal sun shirya karawa da AC milan a cinikin Joshua Zirkzeeda Bologna. (Gazzetta - in Italian)
Dan wasan bayan Real Madrid, Nacho Fernandez ya yanke shawarar raba gari da ƙungiyar a wani mataki da ake zaton zai kai shi ga taka leda a ague Soccer. (Marca - in Spanish)













