Sinadarin vitamin ɗin da 'ya fi ƙara wa' ƙwaƙwalwarku lafiya

Ƙwaƙwalwa

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Da farin farko dai, dole ne mu mayar da hankali kan abincin da muke ci.

Dalilin da ya kamata mu dinga cin ingantaccen abinci shi ne mu tabbatar da cewa mun ci sinadarin vitamin ɗin da ya dace da zai inganta lafiyar jikinmu kuma ya kare mu daga zirarewar ƙwaƙwalwa.

Mu sani cewa akwai sinadaran gina jiki 13 da ke da matuƙar amfani ƙwayoyiyn halitta a jikinmu, game da girma da bunƙasarsu," a cewar cibiyar National Library of Medicine ta Amurka.

Akwai sinadarai da abinci ke ɗauke da su saboda haka yana da kyau mu san abin da muke ɗura wa cikinmu.

"Akwai damar da mutum ke samu a cokalin cin abincinsa," kamar yadda Uma Naidoo ya faɗa wa BBC - wani masanin abinci daga jami'ar Harvard Medical School.

Dr Naidoo ne marubucin "This is Your Brain on Food", wata maƙala da ke bayyana wa mutane abincin da ya kamata su dinga ci don haɓaka lafiyar ƙwaƙwalwarsu.

Maƙalar na ɗauke da jerin abincin da ke cutar da lafiya da kuma wanda ya kamata mutum ya guje wa.

Masana na cewa akwai sinadarin da ya kamata mutum ya riƙe wa wuta, wanda zai taimaka wa lafiyar ƙwaƙwalwarsa.

Wane sinadari ne ya fi taimaka wa ƙwaƙwalwa?

Dr Uma Naidoo

Asalin hoton, Gentileza

Bayanan hoto, Dr Uma Naidoo ƙwararriya ce kan abinci da lafiyar ƙwaƙwalwa a Harvard Medical School

Sinadarin B ne mafi dacewa wajen taimaka wa ƙwaƙwalwar ɗan Adam.

Me sinadarin Vitamin B ke da shi na musamman?

Akwai nau'uka na Vitamin B takwas.

Vitamin B-1: A kan kira shi thiamin, wanda kuma yake ƙunshe da sinadaran da ke taimakawa wajen fitar da abubuwan da jiki ba ya so don taimaka mana wajen bunƙasa.

Ƙarancin thiamin a jikin mutum kan haifar da matsala a ayyukan ƙwaƙwalwa da kuma wasu matsaloli.

Vitamin B-12: Akan kira shi cobalamin. Yana da amfani wajen samar da ƙwayoyin halittar jan jini da kuma na halitta da ake kira DNA. Yana kuma taimaka wa laka da lafiyar ƙwaƙwalwa.

B-12 kan yi abubuwa na musamman, kamar narkar da sinadarin homocysteine da ke haifar wa zuciya matsala - yakan jawo cutar mantuwa.

Ko cin lafiyayyen abinci da yawa zai iya haifar da matsala?

Abincin mai kayan marmari

Asalin hoton, Getty Images

"Sinadarin da na fi son yin magana a kansa shi ne Vitamin B-9, wanda ke ɗauke da sinadarin folic acid (mai ƙara ƙarfin ƙashi)," in ji Dr Naidoo.

"Yana taimaka wa motsin hanyoyin da ƙwaƙwalwa ke aika saƙo da lafiyar ƙwaƙwalwar kanta da ma daidaitonta."

Ɓacin rai na da alaƙa da ƙarancin sinadarin folic acid a jikin mutum.

Yawan cin 'ya'yan itatuwa da ke ƙunshe da Vitamin B-9 a cikinsu na taimaka wa mutane su zauna cikin annashuwa.

Waɗannan na cikin alfanun Vitamin B da aka fi sani da suke da muhimmanci game da lafiyar ƙwaƙwalwarmu.

Duka Vitamin B ne ke taimaka wa ƙwaƙwalwa?

Suna da amfani a sauran jiki fiye da ƙwaƙwalwa kawai, amma duka suna da sinadaran da ke da alfanu ga ƙwaƙwalwar.

"Dalilin da ya sa ke nan idan aka tambaye ni nake ba da shawarar amfani da Vitamin B, saboda wasu na da alaƙa kai-tsaye da ƙwaƙalwa kamar B-12, B-9, B-1. Sauran kuma na tallafa wa ayyukan sauran sassan jiki da suka zama dole kamar samar da jan jini," a cewar Dr Naidoo.

Kai-tsaye ko akasin haka, suna dai da alaƙa da ƙwaƙwalwa.

A ina ake samun sinadarin Vitamin B?

Hatsi, wake, kayan marmari da 'ya'yan itatuwa na da ƙunshe da Vitamin B.

Abin sha na yogurt na da Vitamin B-12 da B-2. Idan mutum zai sha, ana ba da shawarar ya nemi wanda ba shi da sinadaran kamfani sosai.

Irin 'ya'yan itace na cikin manyan hanyoyin samun Vitamin B-5 da ake kira pantothenic acid.

Ana iya samun kashe 20 cikin 100 na wannan sinadari idan mutum ya ci giram 28 na irin 'ya'yan itace.

Ya fi idan mutum ya zuba su a kan abinci ko cikin abin sha.

Ko akwai wata matsala da Vitamin B kan haifar?

Dr Naidoo ya ce: "Idan ana magana kan abinci, ba mu tabbas kan yawan sinadaran da ya ƙunsa, saboda haka nake ba da shawarar a dinga cin daidaitaccen abinci mai kyau."

Ƙwayoyin halittar kowane mutum sun sha bamban da na saura.

Yogurt

Asalin hoton, Getty Images

Mutane na tunanin cewa duk lokacin da aka ace abu yana da alfanu to cinsa da yawa zai ba da fa'ida mai yawa. Wannan kuskure ne.

Cin sinadarai da yawa, ba Vitamin B kaɗai ba, zai iya haifar da matsala, saboda haka a kiyaye.

Dr Uma Naidoo ya ba da shawara kan ƙarin abu biyu:

1. A sha lemon zaƙi (ɓawo) - ba wanda aka sarrafa da sikari ba - saboda yana ɗauke da harza (fiber) da sinadaran gina jiki da sauran ma'adanai da jiki ke buƙata. Lemon zaƙin da aka sarrafa na da sikari sosai kuma an cire harzar da ke cikinsa. 2. Damar da mutum ke da ita tana hannunsa. Abin da mutum yake da iko da shi shi ne kuma abin da ya fi muhimmanci a rayuwarsa.