Mane ba zai buga wa Senegal gasar Kofin Duniya ba

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan gaba na tawagar ƙwallon ƙafa ta Senegal Sadio Mane ba zai buga mata gasar Kofin Duniya ba a Qatar sakamakon raunin da ya ji a gwiwarsa.
A ranar Talata ne hukumar ƙwallon Senegal ta bayyana cewa Mane mai shekara 30 ba zai buga wasannin farko na gasar ba bayan ta saka sunansa a jerin 'yan wasanta duk da raunin da ya ji.
Sai dai hoton gwiwar da aka ɗauka a ranar Alhamis ya nuna cewa akwai buƙatar a yi wa tauraron ɗan wasan tiyata.
Mane ya fita daga wasan da ƙungiyarsa ta Bayern Munich ke fafatwa da Werder Bremen a ranar 8 ga watan Nuwamba sakamakon raunin.
Senegal za ta fara karawa da Netherlands a ranar Litinin a Rukunin A kafin daga bisani ta gwabza da masu masaukin baƙi Qatar ranar 25 ga wata da kuma Ecuador a ranar 29.







