Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ukraine na fuskantar yanayi mafi muni tun fara yaƙinta da Rasha
- Marubuci, Jeremy Bowen
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC international editor
- Aiko rahoto daga, Kharkiv
- An wallafa
Bazara na kunno kai a Ukraine, to amma bisa ga dukkan alamu Kharkiv, birni na biyu mafi girma a ƙasar wanda yake arewa maso gabas kusa da Rasha, ba shi da cikakkiyar kariya daga hare-haren Rasha.
A ranar Asabar kenan lokacin da bama-baman Rasha suka fada kan babban kantin sayar da kaya na DIY, a daidai lokacin da masu siyayya suka yi dafifi.
Yayin da ginin ke cin wuta, manajan ɗaya daga cikin kantinan da ke kusa da wajen Andrii Kudenov, ya rasa yanda zai yi.
“Rashawa suna son su ƙona komai. Amma ba za mu miƙa wuya ba.” In ji manajan.
Wannan dai lokaci ne da mutane ke kula da lambunsu.
Harin da Rasha ta kai ya hallaka aƙalla mutum 15, tare da jikkata gomman mutane, kuma akwai waɗanda ba a gan su ba.
Yayin da tsakiyar birnin inda furanni suke ta ƙone, ana iya ganin iyalai na tafiya da karnukansu. A tsakiyar birnin na Kharkiv, an buɗe shagunan shan gahawa, inda suka yi watsi da jiniyar ankararwa ta hare-hare da ke ta ƙara da kuma wayoyin jama'a da ke yi musu gargaɗi na kai hari.
A gefe daya kana iya ganin matasa maza da mata na ta harkokin wasanninsu da latsa waya suna ɗaukar bidiyon rawa da wasannin da suke yi a TikTok.
A wani ɓangaren kuma mawaƙa na bitar waƙoƙinsu.
Duk da irin yadda matasan ke wannan sha'ani nasu ana iya ganin yadda Ukraine ta kasance a wannan lokaci cikin bala'i mafi muni da ta samu kanta a ciki tun bayan mamayar da Rasha ta yi mata sama da shekara biyu da ta wuce.
Harin da Rasha ta kai a lambun tsakiyar birnin Kharkiv, na daya daga cikin hare-hare mafiya muni da ƙasar ke gani ta fannoni daban-daban.
Ƙarfin Ukraine da kare kanta daga hare-haren ya dogara ne ga matakin da ƙawayenta na yammacin duniya ke ɗauka.
wani abin da ke ƙara sauya yanayin yaƙin kuma shi ne yadda Rasha ke iya jure wa yanayin fagen dagar.
Rasha na ribatar raunin da Ukraine take da shi na kare kanta daga hare-hare ta sama.
Sannan kuma tana da ƙera ƙarin makamai fiye da yadda ƙasashen yamma suke taimaka wa Ukraine.
Fatan da ake da shi na cewa taimakon da Ukraine ke samu zai taimaka mata wajen korar dakarun Rasha, yana dusashewa.
Yanzu dai yaƙin ya shiga shekara ta uku amma kuma ba wata alama ta ganin karshensa da ake iya gani.
Ƙarshen farko?
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi tsammanin samun nasara cikin gaggawa lokacin da ya bayar da umarnin mamayar Ukraine a watan Fabarairun 2022.
Haka ita ma ƙungiyar tsaro ta Nato, bisa jagorancin Amurka ta ɗauka za ta samu galaba a kan Rashar cikin gaggawa.
Gwamnatin Rasha da ta Amurka da sauran ƙasashe na Nato sun yi zaton Rasha za ta iya kammala aikin da ta fara a 2014 lokacin da ta mamayi yankin Crimea ta kuma ayyana samun nasara ta hanyar amfani da ƴan a-ware a lardin gabashi na Donetsk da Luhansk.
Dakarun Ukraine sun ɗan farfaɗo daga irin yadda suke a 2014, to amma bayan nasarar da Rasha ta samu a shiga rikicin Syria da ta yi, hakan ya nuna yadda take da karfi sosai.
Hasashen da dakarun rasha suka yi a Ukraine a watan Fabarairu na 2022 shi ne cewa in har Ukraine za ta iya ci gaba da faɗan to sai dai kawai ta hanyar samar da masu tayar da ƙayar baya a cikin Rasha sda goyon bayan Nato.
Rasha ta kama yankuna da dama a cikin Ukraine da suka haɗa Donbas da ke gabashi da Crimea a kudanci.
To amma yunƙurinta na kama Kyiv ya zamar mata abin kunya ga Shugaba Putin.
Zuwa karshen watan Maris na 2022, dakarun Rasha sun yi rashin galaba a wannan yunƙuri inda suka janye.
Nato ta ga cewa Ukraine za ta iya yaƙin a don haka ne take ci gaba da tallafa mata da makamai a yakin da Rasha.
Duk da cewa Amurka na bai wa Ukraine tallafi sosai a yaƙin to amma Shugaba Biden na fargabar cewa yaƙin duniya na uku na iya ɓarkewa idan ƙasarsa da Nato suka shiga yaƙin kai tsaye ta hanyar bayar da dakarunsu ko kuma suka bai wa Ukraine makamansu na zamani.
Wannan ne ya sa aka shawo kan Shugaba Biden ya yarda Amurka ta taimaka wa Ukraine da tsofaffin jiragen sama na yaƙi, waɗanda Nato ta daina amfani da su.
Rashin miƙa waɗannan jirage ga Ukraine ya bai wa dakarun Rasha damar kai hare-hare.
Yawancin masu fashin baƙi na yammacin duniya suna ganin Shugaba Putin ba da gaske yake ba a kan barazanar amfani da makamin nukiliya.
Babbar ƙawara Rasha wato China ta fito ƙarara ta ce ba ta son a yi amfani da makamin nukiliya.
Har yanzu Joe Biden ba ya son ya tunzura Shugaba Putin a kan wannan barazana ta yin amfani da makamin nukiliya.
Amurkar ya ci gaba da taƙaita amfani da makaman da take bai wa Ukraine taimako, inda take hana amfani da su a kan wuraren da ke cikin Rasha.
Shugaba Zelensky na ganin wannan wani mataki ne na taƙaita amfani da makaman da ake ba shi, abin da yake ta fafutukar ganin Amurkar ta sauya a kai.
Ya zuwa ƙarshen bazara Nato ta tattara manyan makamai na zamani tare da horar da dubban sojoji a kan amfani da makaman.
Nato ta yi hakan ne da zummar ganin bayan Rasha, to amma shirin bai yi nasara ba, domin sojojin Rasha suna da karfi sosai.
Babbar matsalar Ukraine ita ce ta dogara ne ga wasu wajen samun kuɗi da makamai.
Tana yaƙi ne da abokin gabar da yake ƙera makamansa kuma yana da yawan al'umma.
Al'ummar Rasha miliyan 140 ta ninka ta Rasha da kusan kashi uku da rabi.
Wannan kuma abu ne da ke da tasiri a yaƙin da ake dubban jama'a.
A Amurka siyasar cikin gida na taka rawa a yakin na Ukraine.
Bukatar Joe Biden ta bayar da karin tallafi na tsaro da ya hada da dala biliyan 60 ga Ukraine, ta gamu da cikas a majalisar dokokin Amurkar yawqanci daga magoya bayan Donald Trump, wadanda suke son a yi amfani da kudin kan matsalar da take kusa da kasar, musamman ta bakin haure daga iayakar kasar ta kudu, wato Mexico.
Wannan ya sa sai a ranar 24 ga watan Afirilu Shugaba Biden ya sa hannu a kan dokar bayar da tallafin.
Bugu da kari hatta kayan soji na tallafin da Amurkar ke bai wa Ukraine sai an dauki tsawon lokaci kafin su kai ga Ukraine alhalin ita Rasha na kera nata cikin sauri, tare da inganta su.
Wani jami'in Nato ya ce rasha na tsere musu a wannan fanji na samar da makamai wadanda Ukraine ke matukar bukata.
Takunkumin da kasashen yamma suka sanya wa Rasha ya kasa karya tattalin arzikinta, inda a yanzu ta samu sabbin masu sayen mai da iskar gas da take da su.
Haka kuma Rasha ta sayen jiragen sama na yaki marassa matuka daga Iran da kuma harsasai daga Koriya ta Arewa.
Sannan Nato ta yi amman cewa duk da China ba ta taimakon Rasha kai tsaye to amma ta wasu hanyoyin tana taimaka mata.
Garuruwan kan iyaka
Rayuwa a garuruwan da ke kan iyaka tsakanin Rasha da Ukraine na da hadarin gaske, kamar yadda wuta ta tashi a wata makarantar renon yara a kauyen Yurchenkove, da ke arewa da Kharkiv a kusa da iyaka da Rasha.
Sa'ar da aka yi ita ce babu kowa a makarantar a lokacin. Kuma daman garin ya kasance kamar sauran garuruwa na kan iyaka, ba jama'a sosai, sai tsofaffi da sauran farar hula masu rauni.
Rasha na ta kai hare-hare a yankin Kharkiv tun bayan da dakarunta suka tsallaka kan iyakar ranar 10 ga watan Mayu.
Shugaba Putin ya ce shirin shi ne a kafa wani yanki na kare farar hula a Belgorod, birnin Rasha da ke bangaren iyakar inda shugaban ya ce Ukraine na kashe farar hula.
Mun je wannan yanki inda muke hangen Vovchansk, fagen dagar da a yanzu ake fafatwa duk da cewa mun yi nesa-nesa da wurin to amma ko daga inda muke kana iya ganin yadda garin ya zama tarin buraguzai, kuma kana iya ganin hayaki na tashi na sabbin hare-haren bam.
Liubov, ita ce mace ta farko a jerin sunayen mutanen Vika za ta taimaka wa su bar garin.
Matar tana cikin damuwa saboda za ta bar gidan da ta yi sama da shekara 40 tana zaune.
Za ta tashi ne saboda hare-haren bam da ake ta kaiwa.
Sai dai duk da irin hadarin da ke tattare da zama a garin ba kowa ba ne yake yarda ya tashi kamar yadda Vika ta kasa shawo kan Emma da mijnta su tashi.
Maɗaba'a
Kasa da sa'a daya da wani hari na makami mai linzami da Rasha ta kai kan wata maɗaba'a, kana iya ganin wata gawa da aka fita da ita a cikin leda.
Ukraine na cikin tsaka mai wuya saboda karancin hanyoyin da take da su na kariya daga hare-haren sama na Rasha.
Daga irin wannan ne Rashar ta kai hari kan maɗaba'ar, inda harin ya hallaka mutum bakwai.
A harabar madaba'ar yayin da masu kashe gobara ke fama a kan yadda za su kashe wutar tare da neman karin gawarwaki babban jami'in yansanda na na Kharkiv na cike da fushi kan gazawarsu ta kare wadannan hare-hare saboda rashin kayan aiki.
Bayan kwanaki da kai wannan hari daya daga cikin ma'aikatan Olena Lupak, na kwance a asibiti ana yi mata magani.
Olena ta yi amanna tarin takardun da suke aiki da su ne suka kare ta daga wannan hari.
Ta bayyana godiya ga Amurka da Jamus da sauran kasashen duniya da ta ce suna taimaka musu a wannan yaki.
Amma duk da haka tana kokawa da yadda ta ce ba za su iya kare kansu ba.
Kasashen Turai kawayen Ukraine na ci gaba da taimaka wa kasar. sabon tallafin da Amurka za ta ba ta zai taimaka sosai da zaran ya isa.
Hakan na nufin Ukraine za ta iya ci gaba da yakin, sai dai ba fa za ta yi nasara a yakin ba, kuma wannan tallafin shi ne na karshe da Amurka za ta ba ta kafin zaben shugaban kasa a Nuwamba.
Idan Trump ya yi nasa ba a sni ba ko zai matsa kamar yadda Biden yake yi wajen bai wa Ukraine tallafi.
Ita kanta Ukraine din tana taimaka wa kanta wajen bullo da sabbin hanyoyi a yakin inda take amfani da jiragen sama marassa matuka na yaki.
Da amfani da jiragen ruwa marassa matuka makare da bama-bamai, inda ta yi nasarar nutsar da jiragen ruwa na Rasha na yaki.
Yanzu dai Rasha ta yunkuro sosai domin amfani da wannan dama ta yanzu kafin Ukraine ta samu tallafin da aka yi mata alkawari, ta ga ta yi mata illa sosai.
Abin tambaya a na shi ne, ko a wannan bazara Rasha za ta yi amfani da girmanta da karfinta da kuma kwarewarta wajen samun galaba a fagen daga a kan Ukraine, wanda wannan zai iya sauya yadda al'amura suke a yakin.
Ukraine da ƙawayenta suna ganin Rasha ba ta dakarfin da za ta yi abin da ya wuce kama ƴan yankuna a Ukraine, amma kuma da asarar tarin sojoji da makamai.
To amma fa idan aka waiwayi baya shekara daya a lokacin da ake cike da buri a yakin kan hare-haren bazara na Ukraine. A yanzu Rasha ta kara karfi, yayin da za a iya cewa Ukraine ba ta samu wani sauyi sosai ba, kuma Rasha za ta yi duk abin da za ta iya ta kara nasara a yakin.