Manchester United ta hakura da Anthony Martial

Anthony Martial

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Manchester United ta tabbatar da cewar Anthony Martial zai bar ƙungiyar bayan da ƙwantiraginsa zai kare a bana.

Ƙungiyar Old Trafford ba ta amince ta tsawaita yarjejeniyar ɗan Faransa ba, wanda tun farko aka ce za a iya kara masa kaka daya idan ya taka rawar gani.

Martial, mai shekara 28, ya yi kaka tara a United tun bayan da ya koma Old Trafford da taka leda daga Monaco a 2015 da cin ƙwallo 90 a wasa 317.

A kaka uku da ta gabata Martial ya buga wa United wasa 59, daga baya aka bayar da aronsa a rabin kaka a Sevilla, wanda ya zura ƙwallo 12 a raga a Sifaniya.

Rabonda ya buga cikakken wasa a United tun cikin watan Maris ɗin 2021 a FA Cup zagaye na shida da ta yi nasara a kan Leicester City.

Bai buga wasa ba a bana tun bayan da Bournemouth ta doke United 3-0 a Premier League cikin watan Disamba.

Ɗan wasan ya sha fama da jinya, hakan ya sa baya buga wasa da yawa a United da ta kai ta bayar da shi aro ga ƙungiyar dake buga babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Cikin kwallo 90 da Martial ya ci a United, 63 a Premier League ya zura a raga.

Martial ya lashe FA Cup da Carabao Cup da kuma Europa League.

Sai dai bai buga wasa ko ɗaya ba a gasar FA Cup na bana da United ta lashe ba, bayan da ta doke Manchester City 2-1 a Wembley ranar Asabar.

United, wadda ta yi ta takwas a teburin Premier League za ta buga Europa League kai tsaye a badi, sakamakon daukar FA Cup da ta yi.