Newcastle ta koma ta ukun teburin Premier bayan cin Chelsea

Tonali

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Newcastle United ta doke Chelsea 2-0 a wasan mako na 36 a gasar Premier League da suka buga a St James Park ranar Lahadi.

Minti biyu da take lede Sandro Tonali ya fara zura ƙwallo a ragar Chelsea, sannan Bruno Guimaraes ya kara na biyu daf da za a tashi.

Sai dai Chelsea ta karasa karawar da ƴan ƙwallo 19 a cikin fili, bayan da aka bai wa Nicholas Jackson jan kati saura minti 25 su je hutu.

Da wannan sakamakon Newcastle ta koma ta ukun teburi da maki 60 da tazarar maki uku tsakani da Chelsea, wadda take ta biyar a neman gurbin Champions League.

Ƙungiya biyar ce kai tsaye daga Premier League za ta je gasar zakarun Turai a badi daga Ingila.

Ana sa ran za su zama su shida da za su wakilci kasar da zarar an kammala wasan karshe a Europa League tsakanin Tottenham da Manchester United.

Wannan shi ne karo na uku da suka kece raini a tsakaninsu a bana, inda Chelsea ta yi nasarar cin 2-1 a gida a Premier ranar Lahadi 27 ga watan Oktoban 2024.

Newcastle ce ta yi waje da Chelsea a Carabao Cup ranar Laraba 30 ga watan Oktoban 2024 a St James Park.

Kakar 2024/2025

Premier League ranar Lahadi 11 ga watan Mayun 2025

  • Newcastle 2 - 0 Chelsea

English League Cup ranar Laraba 30 ga watan Oktoban 2024

  • Newcastle 2 - 0 Chelsea

Premier League ranar Lahadi 27 ga watan Oktoban 2024

  • Chelsea 2 - 1 Newcastle

Ranar Lahadi Newcastle za ta je Arsenal a wasan mako na 37 da za su kara a Emirates, sannan ta fafata da Everton a wasan karshe a St James Park.

Ita kuwa Chelsea za ta karɓi bakuncin Manchester United ranar Lahadi daga nan ta ziyarci Nottingham Forest a wasan karshe a kakar bana.

Haka kuma Chelsea za ta buga wasan karshe a Conference League da Real Betis ranar 28 ga watan Mayu.

Newcastle tana kan ganiya, bayan da ta lashe League Cup a kakar nan kofin farko a gida tun 1955, kuma na karshe da ta ɗauka a Turai tun Inter-Cities Fairs Cup a 1969.