Abin da zai raba gardama a zaɓen Amurka da kuma dalilin da ya sa ake kankankan a yanzu

    • Marubuci, Anthony Zurcher
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin Arewacin Amurka
    • Aiko rahoto daga, Washington, DC
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

A tarihin siyasar Amurka na baya-bayan nan, ba a taɓa samun sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da ake waswasi a kansa irin na bana ba - wannan ba takara ce ta masu raunin zuciya ba.

Yayin da nasarorin da aka samu a zaɓukan da suka gabata babu tazara sosai - George W. Bush ya yi nasara kan Al Gore ne a shekara ta 2000 da ƴan ɗaruruwan ƙuri'u a Florida - amma a kodayaushe ana ganin alamar inda nasara ta nufa a zaɓen a cikin kwananki kaɗan na ƙarshe.

Wani lokaci, kamar yadda aka samu a 2016, akan samu sauyi a sakamakon da ake tsammani. A waccan shekarar, ƙuri’un jin ra'ayin jama'a sun bai wa Hillary gagarumin rinjaye, kuma ba su yi la'akari da wani yunƙuri da Donald Trump ya yi ba a ƙarshen yaƙin neman zaɓensa.

A wannan karon, alamu na nuni da abubuwa daban-daban. Babu wanda zai iya yin hasashe da gaske kan yadda wannan zaɓe zai kaya.

Kowane ɓangare na iya samun nasara

Galibin ƙuri'un jin ra'ayi na la'akari da yiwuwar samun kuskure a ƙasa baki ɗaya da kuma a muhimman jihohi bakwai da ba su da tabbas da za su yi tasiri kan sakamakon zaɓen.

Dangane da ƙididdiga da yawan ra'ayoyin jama'a da aka saurara, wannan yana nufin kowane ɗan takara zai iya kasancewa a kan gaba.

Wannan rashin tabbas ne ke ci wa masana siyasa da masu kitsa dabarun yaƙin neman zaɓe tuwo a ƙwarya.

An samu ɗimbin abubuwan ban mamaki, da suka haɗa da wani bincike na kwanan nan mai ban mamaki da aka saurari ra'ayin ƴan jam'iyyar Republican a Iowa da ya nuna cewa Harris ce ke kan gaba.

Amma yawancin alƙaluman ƙuri'u suna nuna cewa kowane ɗan takara na iya lashe wannan zaɓe.

Yana yiwuwa a samu wanda zai samu gagarumar nasara

Don kawai sakamakon wannan zaɓen ba shi da tabbas, hakan ba yana nufin ainihin sakamakon ba zai kasance mai fa'ida ba - idan aka samu sauyi na ƴan wasu kaso kaɗan, ɗan takara zai iya lashe zaɓe a duka jihohi masu muhimmnaciu da ba su da tabbas.

Idan aka samu akasi a hasashen masu fitowa jefa ƙuri'a, misali idan mata suka fi yawa a rumfunan zaɓe, ko aka samu mazauna karkara da dama, ko matasa masu jefa ƙuri'a - hakan na iya sauya sakamakon ƙarshe na zaɓen.

Za kuma a iya samun abin mamaki daga ɓangarorin al'umma da ke da matuƙar muhimmanci.

Shin da gaske ne Trump zai iya samun karɓuwa a tsakanin matasa baƙaƙen fata da ƴan Latin Amurka kamar yadda ofishin yaƙin neman zaɓensa ya yi hasashe? Shin Harris na shawo kan mata mazauna yakunan karkara da akasarinsu ƴan republican ne kamar yadda tawagarta ke fata? Shin tsofaffi masu jefa ƙuri'a - waɗanda ke yin zaɓe a kowane zaɓe kuma sukan karkata zuwa gefen masu ra'ayin mazan jiya - za su iya sauya sheƙa zuwa ɓangaren Democrat?

Da zarar an kammala wannan zaɓen , za mu iya yin nuni da dalilin da ya sa ɗan takarar da ya yi nasara ya kasance a kan gaba.

Wataƙila, idan muka yi waiwaye, amsar za ta kasance a fili. Amma duk wanda ya ce ya san yadda al’amura za su kasance a halin yanzu, to yanayaudarar ku ne – har ma da kansa.

jihohi masu launin shuɗi da masu launin ja

A yawancin jihohin Amurka akwai tabbas a sakamakon zaɓen shugaban ƙasa. Sai dai akwai wasu muhimman jahohi guda bakwai da za su matuƙar tasiri a wannan zaɓen.

Ba duk jihohin da ba su da tabbas ba ne ke da matasyi daya ba. Amma kowane ɗan takara yana da wata ''katanga'' ta jihohi uku waɗanda ke kusan tabbatar masa da hanya kai tsaye zuwa fadar White House.

Katangar Harris da ake kira "blue" ko shuɗi, wanda aka danganata da launin Jam'iyyar Democrat, ta mamaye jihohin Pennsylvania da Michigan da Wisconsin a yankin da aka fi sani da ''Great Lakes''. Tun a shekarar 2016 ne lamarin ya ke janyo cece-ku ce, lokacin da Trump ya yi nasara da kyar a dukkan jihohin uku na jam'iyyar Democrat a kan hanyarsa ta samun nasara.

Joe Biden ya yi nasara a waɗannan jihohin shekara ta 2020. Idan har Harris za ta iya riƙe su, ba ta buƙatar wata muhimmiyar jiha kuma, muddin ita ma ta yi nasara a gundumar majalisa a Nebraska (wanda ke da tsarin da ya ɗan bambanta da sauran jihohi wurin bayar da ƙuri'un wakilna masu zaɓenta).

Wannan ya bayyana dalilin da ya sa ta shafe mafi yawan lokutanta a cikin waɗannan jahohin a lokacin yaƙin neman zaɓenta, inda ta shafe kwanaki da dama a kowace jiha.

A daren Litinin, ta gudanar da gangaminta na ƙarshe a Philadelphia da ke jihar Pennsylvania, a saman matakala 72 da ke gaban gidan ajiyar kayan tarihi na birnin, wanda ɗan damben almara na Sylvester Stallone, ya haura a cikin fim mai suna Rocky - kafin ya sha kashi a hannun abokin hamayyarsa, Apollo Creed.

"Katangar'' jihohin masu launin Ja inda Trump ke da tasiri ana samunsu ne ayankin gabashin Amurka. Ba a dai cika magana a kansu ba amma suna da matuƙar muhimmanci a yaƙin neman zaɓensa. Wannan ''katangar'' na farawa ne daga Pennsylvania sai ta yi kudu zuwa North Carolina da Georgia. Idan ya riƙe waɗannan jahohin, zai yi nasara da kuri’un wakilan masu zaɓe biyu na zaɓe biyu, ko da kuwa bai yi nasara a sauran jihohin ba.

Wannan ya bayyana dalilin da ya sa ya gudanar da gangami biyar a North Carolina a cikin makon da ya gabata.

Jihar da ke tsakiyar waɗannan jihohi ita ce Pennsylvania - wadda ita ce babbar kyautar zaɓe a matakin shugaban ƙasa. Shi ya sa ake yi mata da laƙabi da ''Keystone State''.

Ana fafatawa kan makomar Amurka

Wani lokaci tarihin muhimmancin zaɓen shugaban ƙasar Amurka kan ɓata a cikin rububi yayin da ake zana taswirara dabarun zaɓe.

Harris da Trump suna wakiltar ra'ayoyi biyu daban-daban game da Amurka - kan shige da fice da hada hadar kasuwanci da batutuwan al'adu da kuma mu'amalla da sauran kasahen duniya.

Shugaban da zai kwashe shekara hudu masu zuwa yana mulki zai iya tsara gwamnatin Amurka - ciki har da kotunan tarayya - ta hanyar da za ta yi tasiri a cikin shekaru da dama masu zuwa.

Yanayin siyasar Amurka ya matuƙar sauyawa cikin shekaru huɗu da suka gabata, wanda ke nuna sauye-sauyen da ake samu a ɓangarorin al'ummar da ke cikin jam'iyyun biyu.

Jam'iyyar Republican ta shekaru goma da suka gabata ta yi bambanta da jam'iyya mai ra'ayin jama'a da Trump ke jagoranta a halin yanzu, wanda ya fi jan hankalin masu kada kuri'a da ke da ƙaramin ƙarfi.

Har yanzu tushen Jam'iyyar Democrat ya kasance ne kan matasa masu jefa ƙuri'a da mutane da ba fararen fata ba, amma yanzu ya fi dogara kan masu arziki da ilimin kwaleji.

Sakamakon zaɓen bana na iya ba da ƙarin shaida kan yadda waɗannan sauye-sauye a siyasar Amurka, waɗanda aka samu cikin shekaru takwas da suka gabata, ke sake fasalin taswirar siyasar Amurka.

Kuma waɗannan sauye-sauye na iya bai kowane ɓangare galaba a zaɓuka masu zuwa.

Ba da dadewa ba - a cikin shekarun 1970 da 1980 - ana yi wa ƴan Republican kallon waɗanda suka kanannaɗe shugabancin Amurka saboda yadda suka ci gaba da samun rinjaye a jihohi don yin nasara a ƙuri'un wakilan masu zaɓe.

Wannan zaben na iya zama takarar da za ta iya juyawa ga kowane ɓangare amma wannan ba yana nufin hakan ne zai kasance sabon al'adar siyasar shugaban Amurka ba.