Aston Villa ta shirya sayar wa United Watkins, Newcastle na harin Jackson

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester United da Newcastle sun shirya karkata akalasu ga ɗanwasan gaban Chelsea da Senegal mai shekara 24, musamman idan suka gaza ɗauke ɗanwasan gaban Slovenia mai shekara 22 da ke taka leda a RB Leipzig, Benjamin Sesko. (The Athletic - subscription required)

Aston Villa na jiran Manchester United ta gabatar mata da tayi a kan ɗanwasan gabanta mai shekara 29, kuma ɗan Ingila, Ollie Watkins. (Teamtalk)

RB Leipzig ta tuntuɓi Liverpool da tayin ɗanwasan tsakiyar Ingila mai shekara 22, Harvey Elliott, wanda Liverpool ta yi wa farashi £40m (The Athletic - subscription required)

Manchester United ta ƙi amincewa da tayin da ƙungiyoyin gasar Firimiya biyar suka gabatar mata a kan ɗanwasan bayan Ingila mai shekara 32, Harry Maguire. (Mail), external

Juventus ta shirya sayar da ɗanwasan bayan Ingila mai shekara 26, Lloyd Kelly, wanda ta ke sa ran maye gurbinsa da ɗanwasan bayan Arsenal ɗan asalin Poland mai shekara 25, Jakub Kiwior. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Sunderland ta shirya ɗaukar tsohon ɗawasan gaban Everton mai shekara 28, Dominic Calvert-Lewin a kyauta, duk da cewa ɗan wasan Ingilan na fatan jira ko wata ƙungiyar gasar firimiya za ta gabatar da tayi a kansa. (Talksport)

Har yanzu West Ham tana fatan sayen ɗanwasan Aston Villa mai shekara 24, Jacob Ramsey, amma ɗanwasan tsakiyar Ingilan bai yanke hukunci kan yanayin kwangilar da zai sanya wa hannu ba. (Mail)

Newcastle ta shirya gabatar wa AC Milan tayi a kan ɗanwasan bayan Jamus mai shekara 23, Malick Thiaw. (Fabrizio Romano)

Tottenham na son ƙara wa tawagar gabanta ƙarfi , inda ta ke fatan ɗauko ko dai ɗanwasan AC Milan mai shekara 26, kuma ɗan Portugal, Rafael Leao, ko kuma ɗanwasa Real Madrid mai shekara 24, kuma ɗan Brazil, Rodrygo. (GiveMeSport)