Champions League: Kalubalen da ke gaban kungiyoyin Ingila

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Ranar Talata da Laraba za a ci gaba da wasa na bibbiyu a cikin rukuni a gasar zakarun Turai ta Champions League, inda kungiyoyin Ingila za su fafata.

A watan jiya kungiyoyin Premier League biyu suka fara da cin wasannin farko, daya kuma ta yi canjaras, yayin da aka doke daya.

Ranar Talata 19 ga watan Satumba Manchester City ta ci Crvena Zvezda 3 -1 a Etihad, sannan aka tashi babu ci tsakanin AC Milan da Newcastle a Italiya.

Arsenal kuwa cin PSV Eindhoven ta yi 4 -1 ranar Laraba 20 ga watan Satumba, a ranar ce Bayern Munich ta doke Manchester United 4 -3 a Jamus.

Ga jerin kalubalen da ke gaban kungiyoyin Premier a makon nan:

Manchester United da Galatasaray (Talata 3 ga watan Oktoba)

Bruno Fernandes

Asalin hoton, Getty Images

Galatasaray ta samu gurbin shiga gasar Champions League a bana bayan wasannin cike gurbi, wadda ta ci wasa hudu daga biyar, aka saka ta a cikin rukunin farko.

A bara ta lashe kofin Turkiya mai suna Super Lig a karkashin Okan Buruk, wadda ta dauki kofin na 23 jimilla.

Kungiyar ta Turkiya tana da 'yan wasan da suka san gasar Premier kwarai da gaske da za su ziyarci Old Trafford.

Tsohon dan wasan United da Crystal Palace, Wilfred Zaha ya koma Galatasaray kafin fara kakar nan tare da Tanguy Ndombele da Davinson Sanchez daga Tottenham.

Tsohon dan wasan Paris St Germain da Inter Milan, Mauro Icardi shi ne kan gaba a matakin mai ci wa kungiyar kwallaye a Super Lig a bana kawo yanzu, mai bakwai a raga.

Galatasaray tana ta biyu a teburin babbar gasar Turkiya ta kakar nan biye da Fernarbahce, wadda ba a ci wasa ko daya ba a bana.

Galatasaray tana ta uku a rukunin mai maki daya, bayan da ta tashi 2-2 a wasan farko da ta tashi a gida da Copenhagen.

Lens da Arsenal (Talata 3 ga watan Oktoba)

Odegaard

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Lens ta samu shiga Champions League a bana bayan karewa a mataki na biyu a Ligue 1 da tazarar maki daya tsakaninta da Paris St Germain, wadda ta lashe kofin bara.

Kungiyar ta koma kan ganiya, wadda ta kara a Ligue 2 kaka ukun da ta gabata, kafin ta koma buga babbar gasar tamaula ta Faransa.

Duk da kwazon da Lens ta saka a bara, kungiyar na fuskantar koma baya a kakar nan, wadda ke kasan teburi, maki daya ne tsakaninta da Lorient a daf da gurbin 'yan biyun karshe.

Bayan da ta yi rashin nasara a wasan farko a hannun Brest, daga nan ta kasa cin wasa a karawa hudu har da wanda PSG da kuma Monaco suka doke ta.

Sai dai a gasar Champions League da ta fara a bana a karon farko tun bayan 2002, Lens ta samu maki daya bayan tashi 1-1 da Sevilla a cikin rukunin.

Angelo Fulgini ne ya farke musu kwallon da Lucas Ocampos ya zura musu a raga na Sevilla.

Tun daga nan Lens ta ci wasa biyu a jere a Ligue 1 har da wanda ta yi nasara a kan Strasbourg ranar Juma'a.

Newcastle da Paris St Germain (Laraba 4 ga watan Oktoba)

Newcastle

Asalin hoton, Getty Images

Idan Lens ba ta kokari da fara kakar bana, itama Paris St Germain mai rike da Ligue 1 ta fara kakar nan da kafar hagu, wadda ke ta biyar a teburi.

Maki 12 take da shi daga wasa bakwai da ta buga a babbar gasar tamaula ta Faransa da tazarar maki biyu tsakaninta da Monaco mai jan ragama.

Haka kuma ranar Asabar ta tashi canjaras da Clermont Auvergne a gasar ta Ligue 1 karawar mako na bakwai.

Abubwa da yawa sun faru a PSG bayan fara kakar bana, bayan da Lionel Messi ya koma buga gasar Amurka a Inter Miami, sannan aka maye gurbin kociya, Christophe Galtier da Luis Enrigue, tsohon wanda ya horar da Barcelona da tawagar Sifaniya.

Haka kuma Neymar ya koma buga gasar Saudiyya a kungiyar Al Hilal, yayin da aka samu rashin jituwa kan tsawaita kwantiragin Kylian Mbappe.

Daga baya an kamo bakin zare har ya koma atisaye da buga wa kungiyar wasanni, wanda tun farko ke fatan komawa Real Madrid a kaka mai zuwa

Da fara kakar nan PSG ta yi canjaras biyu wadda daga baya ta sa kwazo ta yi nasara a wasa uku, amma ta fara da cin wasan farko a rukuni na shida.

Kungiyar Faransa ta yi nasara a kan Borussia Dortmund da cin 2-0, inda Kylian Mbappe da Achraf Hakimi suka ci mata kwallayen.

RB Leipzig da Manchester City (Laraba 4 ga watan Oktoba)

Man City

Asalin hoton, Getty Images

Mai rike da Champions League, Manchester City za ta ziyarci RB Leipzig ranar Laraba, bayan da suka ci wasansu na farko a cikin rukuni na bakwai.

Kungiyar Jamus ta fara da taka rawa mai kyau, bayan doke Young Boys 3-1, inda Mohamed Simakan da Xaver Schlager da kuma Benjamin Sesko suka ci mata kwallayen.

To sai dai Leipzig na fatan kada a kara zura mata kwallaye da yawa kamar yadda City ta yi mata a bara a gasar a zagayen kungiyoyi 16.

City ta doke Leipzig 7-0, inda Erling Haaland ya ci biyar daga ciki da kai wa zagayen gaba da cin kwallo 8-1 a haduwa gida da waje.

A yanzu haka Leipzig tana ta biyar a kan teburin Bundesliga, wadda Bayern Munich ta taka mata burki a karshen mako da suka tashi 2-2, bayan da ta ci wasa hudu a jere.

Wasa daya ta yi rashin nasara a hannun Bayer Leverkusen a ranar fara Bundesliga, yanzu haka da tazarar maki uku tsakaninta da wadda take ta daya a teburi.