Moyes ya kasa cin Chelsea a Stamford Bridge karo na 18

David Moyes

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Chelsea ta doke West Ham da ci 2-1 a wasan mako na shida da suka buga a Stamford Bridge ranar Asabar.

West Ham ce ta fara cin kwallo ta hannun Michail Antoni a zagaye na biyu, bayan da suka tashi ba shi a minti 45 din farko.

Kwallon farko kenan da Antonio ya ci wa West Ham a Premier a kakar nan, bayan buga aka yi wasa shiga da fara kakar bana.

Daga baya Chelsea ta farke ta hannun Ben Chilwell, sannn Kai Havertz ya kara na biyu saura mini biyu a tashi daga karawar.

Wannan shi ne wasa na 18 da David Moyes ya je Stamford Bridge amma bai yi nasara ba.

Wasan farko da West Ham ta buga ranar Asabar tun bayan 5 ga watan Maris, wadda ta yi karawa 14 da daya a ranar Laraba tun daga lokacin.

Kawo yanzu West Ham ta ci wasa daya da canjaras 1 da shan kashi a fafatawa hudu da maki hudu kenan.

West Ham za ta karbi bakuncin Steau Bucarest a wasan farko na cikin rukuni a Europa Leageu ranar 3 ga watan Satumba.

Chelsea kuwa ta hada maki 10, bayan cin karawa uku da canjaras daya da rashin nasara a wasa biyu.

Ranar 6 ga watan Satumba Chelsea za ta ziyarci Dinamo Zagareb a wasan farko a cikin rukuni a Champions League.