Kyaftin Nacho ya bar Real Madrid bayan shekara 23

An wallafa

Kyaftin ɗin Real Madrid Nacho ya bar ƙungiyar bayan lashe kofuna 26, ciki har da na zakarun Turai shida.

Ɗan Sifaniyan mai shekara 34 ya je makarantar koyon ƙwallo ta Real yana da shekara 10, inda daga baya ya buga wa babbar ƙungiyar wasa 364 tun daga 2012.

Wasansa na ƙarshe shi ne karawar da Real ta doke Borrusia Dortmund 2-0 kuma ta wawure kofin Champions League a watan da ya gabata - kuma ya zama cikin 'yan wasa biyar da suka ci kofin sau shida a kulob ɗin.

Nacho da ke buga wa Sifaniya gasar Euro 2024 a yanzu, ana sa ran zai koma kulob ɗin Al-Qadsiah na Saudiyya.

"Na shafe watanni ina ta tunani, taraddadi da kuma kokwanto, amma yanzu ina shaida muku cewa za mu fuskanci wani sabon ƙalubalan ni da iyalina,," in ji Nacho.

Ya buga wa ƙasarsa Sifaniya wasa 26.

Ya kuma ci La Liga huɗu tare da Real, Spanish Cup biyu, Kofin Duniya na Kulob biyar, European Super Cu huɗu, da Spanish Super Cup biyar.

Shugaban Real Florentino Perez ya ce: "Tun daga lokacin da ya zo kwalejin matasa, Nacho ya kasance abin misali, da koyo, da ƙauna ga kowa."