Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Atalanta ta yi wa Ademola Lookman farashi, Atletico na zawarcin Romero
Atletico Madrid ta nuna sha'awar sayen ɗanwasan Tottenham mai shekara 26, Cristian Romero. (Sky Sports)
Everton ta shirya tsaf domin soma tattaunawa da ɗanwasan Ingila Jarrad Branthwaite, mai shekara 22, kan sabuwar yarjejeniya domin katse hanzarin wasu ƙungiyoyin. (I Sport)
Manchester United za ta nemi ƙulla yarjejeniya da Branthwaite ne kawai idan ɗanwasan Ingila Harry Maguire mai shekara 32, ya bar Old Trafford. (Yahoo)
Arsenal a shirye take ta yi wa Gabriel, mai shekara 27 tayi domin daƙile sha'awar ɗaukan ɗanwasan daga Saudiyya. (Football Insider)
Ita ma Real Madrid ta bayyana sha'awar ɗaukan ɗanwasa William Saliba mai shekara 24, wanda abokin wasan Gabriel ne a Arsenal. (Mirror)
A gefe guda kuma Arsenal ta bi sahun Liverpool a zawarcin ɗanwasan Netherlands mai shekara 19 Jorrel Hato daga Ajax. (Team talk)
Atalanta na shirin karɓar fam miliyan 50 kan Ademola Lookman mai shekara 27, daidai lokacin da Manchester United da Newcastle United ke zawarcinsa. (Tuttomercato – in Italian)
Aston Villa ta soma tattaunawa da ɗanwasan tsakiya na Faransa Boubacar Kamara, mai shekara 25, game da ƙulla sabon kwantiragi. (Telegraph)
Yarjejeniyar da Barcelona take da shi da Sporting Lisbon na sake sayen ɗanwasan Portugal mai shekara 25 Francisco Trincao, wanda ke da alaƙa da Manchester United da Arsenal da Newcastle ta ƙare a Yunin 2024. (Record - in Portuguese)
Crystal Palace na samun nasara a tattaunawar da take game da sabon kwantiragi na koci Oliver Glasner, yayin da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta RB Leipzig ita ma take zawarcin ɗan ƙasar ta Austriya. (Football Insider)