Champions League:Man City da Real Madrid sun kai zagayen dab da na kusa da karshe

An wallafa

Manchester City za ta sami ƙwarin gwiwa yayin da ta ke shirin fafatawa da Liverpool a gasar premier league a ƙarshen mako bayan ta yi nasarar tsallakawa zuwa zagayen daf da na kusa da ƙarshe a gasar Zakarun Turai (Champions League) a karo na bakwai a jere.

City ta doke FC Copenhagen da ci 3-1 a wasan da aka buga a filin Etihad.

Bayan ta ci wasan farko a gidan Copenhagen da ci 3-1, City ta jefa ƙwallo biyu a raga a minti tara na farkon wasa ta hannun Manuel Akanji da Julian Alvarez.

Erling Haaland ya ƙara ƙwallo ta uku a ƙarshen rabin lokaci na farko bayan Elyounoussi ya farke wa Copenhagen ƙwallo ɗaya a minti na 29.

A ɗaya wasan zagaye na biyu da aka buga a daren na Laraba, Real Madrid ta sha da ƙyar inda ta yi canjaras da RB Leipzig da ci 1-1, a wasan da aka buga a filin wasan Santiago Bernabeu.

Amma Madrid ta ƙetara sakamakon nasarar da ta yi a wasan farko a gidan Leipzig da ci ɗaya mai ban haushi.

Vinícius Júnior ya fara jefa ƙwallo a raga a minti na 65 kafin Willi Orbán ya farke wa Leipzig a minti na 68.

A halin yanzu ƙungiyoyi hudu ne suka ketara zuwa zagaye na gaba a gasar bana, bayan Bayern Munich da PSG sun yi nasara a wasannin da aka buga a daren ranar Talata da ta gabata.

Za a kammala wasannin zagaye na biyu a mako mai zuwa inda za a tabbatar da ƙungiyoyin da za su kasance a zagayen ƴan takwas na ƙarshe.