Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Babu matsala tsakanina da Enrique - Mbappe
Ɗan wasan gaba na Paris St-Germain Kylian Mbappe ya ce "ba shi da matsala" da koci Luis Enrique bayan da ya zura ƙwallaye biyu a gasar cin kofin zakarun Turai da suka doke Real Sociedad wanda hakan ya sanya PSG ta ƙetara zuwa zagayen daf da na kusa da na ƙarshe.
Ɗan wasan na Faransa ya nuna bajinta yayin buga cikakken wasan minti 90 na farko tun ranar 14 ga Fabrairu.
Matsayin Mbappe a PSG ya yi matuƙar jan hankali, bayan da ɗan wasan ya amince ya koma Real Madrid a wannan bazarar.
Tun bayan da ya bayyana aniyarsa ta barin Parc des Princes, masu bibiyar harkar ƙwallon ƙafa sun sanya alamar tambaya kan zamantakewarsa da Enrique, inda ake ajiye ɗan wasan a benci ko kuma an cire shi da wuri, musamman wasannin PSG uku na baya-bayan nan a gasar Ligue 1.
"A koyaushe ina son buga gasar zakarun Turai, gasa ce mai matuƙar muhimmanci. Ba zan taɓa zama ɗan wasan da ke ɓuya ba," in ji Mbappe.
Ya ƙara da cewa, ''Dangantaka ta da kocina na da kyau, babu matsala ko da mutane za su yi tunanin cewa akwai. Ina da matsaloli da yawa amma kocin ba ya cikinsu."
Da aka tambaye shi game da sauya Mbappe a wasannin baya, koci Enrique ya ce: "Kylian zai zura ƙwallaye 50, ya kuma taimaka a ci 25 da kowane koci, a kuma kowace ƙungiya.
"Tabbas, makomarsa ba za ta kasance tare da mu ba don haka dole ne mu nemi mafita."