Babu wani 'sihiri' da zai magance matsalolin United - Solskjaer

An wallafa

Tsohon kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya ce babu “wani sihiri” da zai iya kawar da matsalolin da ke addabar ƙungiyar.

Sir Jim Ratcliffe ya sayi hannun jarin kashi 27.7 cikin ɗari a United, wadda ta sha kashi a hannun Manchester City da ci 3-1 ranar Lahadi.

Wannan ne karo na 11 da United ta yi rashin nasara a gasar Premier League a bana kuma ƙungiyar Erik ten Hag ta kasance ta shida a kan teburi.

Solskjaer ya ce ''Ina fatan Erik zai yi nasara. Ina matuƙar fatan haka amma ba za ka san irin tunanin da sabbin masu mallakar ƙungiyar za su yi ba."

"Ya danganta da sakamako da kuma daidaito a sauran wasannin da suka rage a kakar wasa."

Ratcliffe ne zai kula da ɓangaren ƙwallon ƙafa na kulob ɗin, amma dangin Glazer za su ci gaba da kasancewa masu rinjaye.

Attajirin na Birtaniya ya yi kira ga magoya bayan ƙungiyar da su ƙara hakuri kuma ya shaida wa BBC cewa: "Muna buƙatar mutane su ba mu lokaci don mu dawo kan ganiyarmu. hakan na iya ɗaukan kakar wasa biyu zuwa uku."

Da yake magana da manema labarai, Solskjaer mai shekaru 51, wanda ya jagoranci United daga 2018-21, ya ƙara da cewa: "Ba na tsammanin akwai wani sihirin da za a yi amfani da shi, kamar sauya mamallaka.''

Akwai tazarar maki 19 tsakanin United da Liverpool wadda ke jagorantar gasar Premier ta bana sannan tana bin Aston Villa da maki 11 wadda ke matsayi na huɗu.

Da alama Gasar FA Cup ce kaɗai damarta ɗaya tilo na lashe kofi a bana , kuma za ta kara da Liverpool a wasan zagayen quater Final ranar Lahadi, 17 ga Maris.