An kaddamar da Shirin Mata 100 Na BBC karo na 10

Wata fitacciyar ma'aikaciyar lafiya 'yar kasar Ukraine da wata 'yar kasar Iran da ke zanga-zanga, wadda muka sakaya sunata, na cikin jerin matan da suka suka shiga shirin Mata 100 na BBC 2022.
Matan da suka samu kansu a wannan shirin suna cikin wadanda suka karade kanun labarai na duniya, cikin su har da matar shugaban Ukraine Olena Zelenska da kuma 'yar kasar Iran da ta yi fice wurin hawa tsauni Elnaz Rekab, wadda ta shiga gasar hawa tsauni ba tare da dan kwali ba a yayin da ake zanga-zanga a kasar domin kyamar sanya hijabi.
Mawaki kuma mai rubuta wakoki 'yan kasar Amurka Billie Eilish da fitacciyar tauraruwar fina-finan Indiya Priyanka Chopra Jonas na cikin matan da aka karrama a wannan shiri saboda rawar da suka taka wurin inganta rayuwar al'ummar duniya.
An kaddamar da shirin Mata 100 domin jawo hankali game da fito da labaran da suka shafi mata bayan wani gungun bata-gari a birnin Delhi ya rika yi wa mata fyade a 2012.
Wannan ne karo na 10 da ake gudanar da shirin, kuma maudu'in shekarar 2022 shi ne "ci gaba" da kuma yin waiwaye kan sauye-sauyen da aka samu a shekaru goma da suka gabata. Za a kwashe mako daya ana gudanar da hirarraki da bayanai da rahotanni na intanet a Sashen BBC na Birtaniya da kuma mai watsa shirye-shiryen talabijin, rediyo, intanet da BBC iPlayer a kasashen duniya.
Baya ga hira da za a yi da Eilish, Shirin na BBC 100 Women ya yi tattaunawa ta musamman da Chopra Jonas, da mai fafutukar kare hakkin masu bukata ta musamman Selma Blair da kuma tauraruwar fina-finan Amurka Rita Moreno.
Za a wallafa hirarrakin a BBC iPlayer, BBC World News, and BBC.co.uk/100women.
Kazalika za a gabatar da shirye-shirye na musamman na yanzu da wadanda suka gabata game da ire-iren cin zarafin da aka yi wa mata.
A karon farko, an bai wa matan da a baya suka shiga shirin na 100 damar bayar da sunayen wadanda za a iya zaba domin zama gwarazana mata na wannan shekarar.
Alal misali, matashiyar nan da ta lashe kyautar Nobel kan zaman lafiya Malala Yousafzai, ta mika sunan Alice Pataxó, mai fafatukar kare muhalli kuma 'yar jarida 'yar kasar Brazil.
Darakta Janar na BBC Tim Davie ya ce: "Matan da ke cikin jerin wadanda za a karrama a wannan shekarar yana da ban sha'awa saboda sun yi nasara kuma sun bayar da gudunmawa a al'ummarsu, kuma ina alfahari game da yadda BBC ke ci gaba da ayyuka na musamman do,min fito da su da bayar da labaransu ga duniya."











