Man United da Barca: Wa zai kai zagayen gaba a Europa?

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United za ta kara da Barcelona a Old Trafford ranar Alhamis a wasa na biyu a neman shiga gurbin 'yan 16 a Europa League.
A makon jiya kungiyoyin suka tashi 2-2 a Camp Nou ranar 16 ga watan Fabrairu a Sifaniya.
United, wadda rabon ta dauki kofi tun 2017 za ta buga wasan karshe a Caraboa Cup ranar Lahadi a Wembley da Newcastle United.
Kungiyar Old Trafford tana ta ukun teburin Premier League da tazarar maki biyar tsakaninta da Arsenal ta daya.
United za ta fafata da West Ham United a zagaye na biyar a FA Cup ranar 1 ga watan Maris.
Barcelona tana ta daya a teburin La Liga da tazarar maki takwas tsakaninta da Real Madrid ta biyu.
Karo na 14 da suka kara a tsakaninsu, inda Barcelona ta yi nasara a shida da canjaras biyar, United ta ci uku.
'Yan wasan Barcelona da aka je da su Old Trafford:
Ter Stegen, R. Araujo, Sergio, Lewandowski, Ansu Fati, Ferran, Christensen, Marcos A., Jordi Alba, Kessie da kuma S. Roberto.
Sauran sun hada da F. De Jong, Raphinha, Kounde, Eric, Iñaki Peña, Balde, M. Casadó, Pablo Torre da kuma Arnau Tenas.
Wasa 14 tsakanin Barcelona da Manchester United:
2022/23 Champions League
- Barcelona 2 - 2 Man United
2018/2019 Champions League
- Barcelona 3 - 0 Man Utd
- Man Utd 0 - 1 Barcelona
2010/2011 Champions League
- Barcelona 3 - 1 Man Utd
2008/2009 Champions League
- Barcelona 2 - 0 Man Utd
2007/2008 Champions League
- Man Utd 1 - 0 Barcelona
- Barcelona 0 - 0 Man Utd
1998/1999 Champions League
- Barcelona 3 - 3 Man Utd
- Man Utd 3 - 3 Barcelona
1994/1995 Champions League
- Barcelona 4 - 0 Man Utd
- Man Utd 2 - 2 Barcelona
1990/1991 Euro Cup Winners Cup
- Man Utd 2 - 1 Barcelona
1983/1984 Euro Cup Winners Cup
- Man Utd 3 - 0 Barcelona
- Barcelona 2 - 0 Man Utd










