Chelsea ta sallami Graham Potter

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea ta sallami Graham Potter, bayan wata bakwai yana jan ragamar ƙungiyar ta Stamford Bridge.
Ranar Asabar ne, Aston Villa ta doke Chelsea 2-0 a wasan mako na 29 na Gasar Premier.
Wasa na 11 da aka doke Potter a cikin karawa 31 da ya yi jagoranci tun bayan maye gurbin Thomas Tuchel a Stamford Bridge ranar 8 ga watan Satumba.
Chelsea, wadda ta kashe sama da fam miliyan 550 wajen sayo sabbin 'yan wasa, za ta ɗauki wani kocin a kakar nan.
The Blues tana ta 11 a teburin Premier da ratar maki 12 tsakaninta da kulob ɗin da ke matsayi na huɗun ƙarshe a kakar bana.
Chelsea ta ce ''Potter ya ba da haɗin kai ga ƙungiyar don naɗa wanda zai kai kulob ɗin matakin gaba'' Bruno Saltor ne zai yi aikin riƙon ƙwarya.
Chelsea za ta karɓi baƙuncin Liverpool a Premier League ranar Talata, kafin ta je ta buga wasan farko da Real Madrid a karawar daf da kusa da ta ƙarshe ranar 12 ga watan Afirilu a ƙasar Sifaniya.
Kawo yanzu, an kori koci 12 a Gasar Premier cikin wannan kakar wasanni, amma idan ka haɗa da komawar Potter zuwa Chelsea daga Brighton, sun zama 13 kenan.
Potter ya taka rawar gani a Brighton, inda a tsawon kaka uku ta Gasar Premier, ya kai ƙungiyar mataki na tara, gurbi mafi ɗaukaka da ta taɓa takawa kafin lokacin.
Hakan ya sa aka yi ta yabon kocin da salonsa na horarwa, da yadda ƙungiyar ke murza leda, da yadda yake ɗaukar matasan 'yan ƙwallo.
Brighton na mataki na huɗu a teburin Firimiya lokacin da Chelsea ta ɗauke shi aiki a watan Satumba.
Tun bayan barin Brighton, ƙungiyar ta ci gaba da taka rawar gani a ƙarƙashin sabon koci, Roberto de Zerbi wanda ke ƙoƙarin kai kulob zuwa Gasar Zakarun Turai a shekara mai zuwa.











