Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hukumomin Syria sun ce magoya bayan Assad sun kashe jami'an tsaronsu 14
Sabuwar ma'aikatar kula da harkokin cikin gida ta Syria ta ce an kashe jami'anta 14 aka kuma raunata 10 a wani kwanton-bauna da mabiya akidar Shi'a ta Alawite da hambararren shugaban kasar Bashar al-Assad ke bi suka yi musu a yankin yammacin kasar.
Hukumomin sun ce an yi dauki-ba-dadi ne a kusa da tashar jirgin ruwa ta tekun Bahar-Rum a birnin Tartous a ranar Talata.
Rahotanni sun bayyana cewa an yi wa jami'an tsaron ma'aikatar cikin gidan wannan ta'annati ne lokacin da suka je domin kama wani cikin tsofaffin manyan jami'an da ke da alaka da gidan yarin nan na Saydnaya, da ke kusa da babban birnin kasar Damascus.
Gidan sarkar da ya yi kaurin suna wajen azabtarwa da gana akuba ga tsararru a lokacin mulkin Assad.
An yi wa jami'an tsaron sabuwar hukumar kasar ta Syria karkashin ‚yan tawayen kungiyar Hayat Tahrir al-Sham (HTS), wannan ta'annati ne sama da mako biyu kacal da suka hambarar da gwamnatin Shugaba Assad, wanda ya yi shekara 24 yana jagorantar kasar bayan mulkin da mahaifinsa Hafez al-Assad ya yi na shekara 30, tun daga juyin mulkin 1970.
Shigar sauri da mayakan kungiyar 'yan tawayen ta HTS suka yi da hare-hare daga arewa maso gabashin kasar ta Syria inda nan da nan suka mamaye kusan kasar baki daya ya kawo karshen mulkin iyalan Assad na sama da shekara hamsin.
Daga nan ne Shugaba Assad da iyalinsa suka tsere zuwa Rasha.
Kungiyar da ke sa ido kan batutuwan kare hakkin dan'Adam a Syria wadda ke da mazauni a Birtaniya ta ce a yayin kwanton-baunar da aka yi wa jami'an ma'aikatar cikin gidan na Talata, su ma maharan sun rasa mutun uku.
Ta ce daga baya sababbin hukumomin na Syria sun samu daukin karin jami'an tsaro.
Kungiyar HTS da ta hambarar da shugabancin na Assad, tun bayan da ta dare kan mulki ta yi alkawarin kare ‚yancin kungiyoyin addinai da kabilu marassa rinjaye a kasar ta Syria.
Tun a baya Majalisar dinkin Duniya da Tarayyar Turai da Amurka da Birtaniya da sauransu sun ayyana kungiyar ta HTS, mai da'awar jihadi a matsayin kungiyar ta'addanci.
A ranar Talata zanga-zanga ta barke a kasar ta Syria saboda kona bishiyar Kirsimeti, abin da ya kara taso da kira ga sababbin hukumomin masu ikon na Syria da su tashi tsaye kann kare 'yanci da hakkin tsiraru a kasar.