Nottingham Forrest ta kammala ɗaukar Jota Silva

...

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Nottingham Forest ta kammala sayen ɗan wasan gaban Portugal Jota Silva daga Vitoria Guimaraes kan kwantiragin shekara huɗu.

Ɗan wasan mai shekara 25, ya zura ƙwallaye 15 kuma ya kuma taimaka aka zura ƙwallaye bakwai a dukkan gasa a bara.

Ya buga wasansa na farko a tawagar Portugal a watan Maris kuma ya zuwa yanzu ya buga ma ta wasanni biyu, amma bai sami shiga tawagar ƙasar da ta buga gasar Euro 2024 ba.

Forest ta ƙare a mataki na 17 a gasar Firimiya a kakar wasan da ta gabata, inda maki shida ne kacal suka hana ta faɗawa gasar Championship.

Har ila yau ƙungiyar ta sayi ɗan wasan baya Nikola Milenkovic daga Fiorentina ta kuma ɗauki ɗan wasan tsakiya Elliot Anderson daga Newcastle United a wannan bazarar.