Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Taimako biyar da ya kamata ku bai wa wanda ya yanke da wuka a gida
- Marubuci, Aisha Babangida
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Jorunalist
- Marubuci, Aisha Babangida
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Jorunalist
- An wallafa
"Wani abun taƙaici shi ne yadda wasu mutane ke ƙoƙarin ɗaukar hoto a lokacin da aka samu hatsari na yanka ko sukar wuƙa ko da wani makami mai tsini ko kuma idan a gida hatsarin ya faru, ka ga wasu su yi ta sama da ƙasa su rasa yadda za su yi a maimakon su koyi matakai na gaggawa domin ceton rai."
Wannan ita ce kalmar dakta Shuaibu Musa, ƙwararren likita a asibitin koyarwa na Barau Dikko da ke jihar kaduna a lokacin da yake tattanawa da BBC.
Likitan ya ce irin wannan lamari ba ƙaramin bala'i ba ne, inda ya ce ihu ba shi da muhimmanci, kuma ba ya tsayar da jini ko kuma kare rai, saboda haka, ya kamata mutane su san matakan da za su taimaka wajen ceton rai saboda shi ne babban abun da ya dace.
A cikin ayyukanmu na yau da kullun, hadurra na iya faruwa ba zato ba tsammani, kamar hatsari na yankan wuƙa ko ƙwalba ko kuma wani abu mai kaifi a gida, ko ofishi, ko kasuwa, ko wajen taro, ko kuma wajen da mutane ke faɗa da junansu da makamai masu kaifi, da dai sauransu.#
Hakan ka iya jefa mutum cikin wani mummunan hali ko ma ga mutuwa saboda tsananin zubar da jini idan har bai sami taimakon farko ba ko makamancin hakan.
Mutane da dama da ke wurin da irin wannan hatsarin ke faruwa suna samun kansu cikin rashin tabbas game da abin da za su yi domin tsayar da jini ko irin taimakon farko da ya kamata su bayar.
Matakai biyar domin ceton rai?
Dokta Musa ya ce matakan da mutane ya kamata su sani idan aka samu hatsari na yankan wuƙa, ko reza ko kuma wani abu mai tsini a hannu ko ƙafa, ko wani ɓangare na jiki ta yadda aka yanki jijiya kuma jini na zuba a gida ko a wurin aiki, ko a wani wuri dai ba wasu matakai ba ne da yawa.
Ya ce sanin matakan da kuma iya aiwatar da su yana da muhimmanci sosai domin za su iya ceton rai kuma idan har ba a san su ba balantana awaitar da su to zai iya kai wa ga mutuwa.
- Saka karfi: Wannan dai na nufin sanya karfi a danne wurin da aka samu yankan na hannu ta yadda zai hana jini fita, ko kuma inda yankan babba ne. Ya kara da cewa mutum ya nemi wani zani ko danƙwali ko wani hankacif, ko wani ƙyalle dai mai tsafta ya danne gurin yankar da ƙarfi sosai har sai ya tabbatar da jinin ya daina zuba sosai daga nan sai a gaggauta kai wanda ya sami raunin asibiti.
- Daga wurin yankan sama: idan wurin da aka samu yankan na iya ɗaguwa kamar a hannu, ko ƙafa haka, toh ya kamata a ɗaga sama saboda hakan zai saka jinin ya daina zuba. Idan kuma a gefen ciki ne, wanda ya samu raunin zai kwanta akan ɓangaren da ba na raunin ba yadda waje mai raunin zai kasance a sama, ko kuma idan a baya ne, toh, wanda ya sami raunin zai yi rub-da-ciki yadda bayan zai kasance a sama, ta haka, jinin zai iya daina zuba sai kuma a haɗa da mataki na farko na dannewa.
- Ka da a ringa yawo: Mataki na uku shi ne a tabbatar kar a dinga yawo da wanda ya sami raunin, ko kuma jijjiga shi ko motsa shi zuwa wurare, domin hakan yana ƙara saka jinin ya ƙara zuba da ƙarfi, saboda haka, ya kamata a bar shi a guri ɗaya, sai a gwada amfani da mataki na ɗaya ko na biyu da aka lissafo daga nan kuma sai a gaggauta kai mutum asibiti.
- Daure rauni: Dakta Musa ya ce wani matakin kuma na taƙaita zubar da jini shine a bin da ake kira da 'Tourniquet dressing". Shi dai tourniquet dressing shigen matakin farko da aka lissafo ne amma sai dai shi wannan ana amfani da wani ƙyalle ko igiya ko zare ko roba haka a daure saman inda ciwon yake da ƙarfi, ko kuma ana iya amfani da su hade da wani ludayi ko ɗan sanda a ɗaure saman wurin da ciwon yake yadda ba zai iya ƙwancewa ba, idan aka yi hakan, to, tabbas jini zai daina zuba.
- Gaggauta zuwa Asibiti: Mataki na biyar kuma da mutane ya kamata su sani idan har an gwada aiwatar da matakan da na lissafo shi ne a gaggauta kai wanda ya sami raunin zuwa asibiti saboda a can ne za a iya yin gwaje-gwaje a gano abin da ya sa jinin ya ƙi tsayawa.
Daga karshe dai likitan ya kuma bayar da shawarar cewa idan aka samu irin wannan hatsari na yankan abu mai tsini, toh mutanen da ke wurin su dage wajen kwantar da hankalinsu da kuma wanda ya samu raunin ba tare da nuna firgici ba ko kuma nuna wa wanda ya sami raunin cewa zai iya mutawa ko kuma ciwon nasa sai a hankali da dai sauransu.