Arsenal na son Lamine Yamal, Real Madrid da Chelsea na zawarcin Davie

Lamine Yamal

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Lamine Yamal
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester United na tattaunawa da 'yan takarar kocinta domin maye gurbin Erik ten Hag, Kevin de Bruyne zai iya barin Manchester City zuwa gasar Major League Soccer, Eintracht Frankfurt ta sanar da farashin da take son sayan dan wasan Liverpool Omar Marmoush.

Tuni dai Manchester United ta tattauna da 'yan takarar zama kocinta da dama yayin da dan kasar Holland Erik ten Hag ke ci gaba da fuskantar matsin lamba. Wadanda aka tattauna da su sun hadar da Xavi Hernandez da kocin Sporting Lisbon Ruben Amorim. (Daily Mail)

Dan wasan tsakiya na Manchester City Kevin de Bruyne, mai shekara 33, zai iya komawa kungiyar kwallon kafa ta Major League Soccer inda San Diego FC ke nemansa, yayin da kwantiragin dan kasar Belgium din zai kare a watan Yuni. (GiveMeSport)

Eintracht Frankfurt tasamya farashin Yuro miliyan 50 zuwa 60 wato (£41.6m-50m) a matsayin abun da za ta iya sayar da dan wasan gaban Masar Omar Marmoush mai shekaru 25, wanda wakilansa suka tattauna da Liverpool. (Sky Germany)

Arsenal ta fitar da jerin sunayen ‘yan wasan gaba na duniya da take son dauka, ciki har da dan wasan Newcastle da Sweden Alexander Isak, mai shekara 25, kuma shine ma kan gaba a jerin. (TeamTalk)

Inter Milan na zawarcin dan wasan tsakiyar Athletic Bilbao, mai shekara 24, dan kasar Sipaniya Oihan Sancet, wanda kuma Aston Villa ke zawarcinsa. (Fichajes Spanish)

Tottenham ta kuduri aniyar hana Pedro Porro mai shekara 25 dan kasar Sipaniya komawa Manchester City, wanda ake ganin zai maye gurbin Kyle Walker mai shekara 34. (Football Insider)

Liverpool da Arsenal suna fafatawa don siyan dan wasan Spain da Barcelona Lamine Yamal, mai shekara 17, saboda kungiyar ta La Liga za ta iya sayar da matashin dan wasan gaban saboda matsalolin kudi. (Miguel Delaney )

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dan wasan Brazil Raphinha, mai shekara 27, ya ce ya yi tunanin barin Barcelona fiye da sau daya a kakar wasanni biyun farko da ya yi da kulob din bayan ya koma Leeds. (ESPN)

Liverpool na shirin daukar dan wasan bayan Celta Vigo dan kasar Sipaniya Oscar Mingueza, mai shekara 25, domin maye gurbin Trent Alexander-Arnold dan kasar Ingila, mai shekara 26. (Fichajes Spanish)

Manchester United na son dauko dan wasan Sunderland dan kasar Ingila Chris Rigg, mai shekara 17. (GiveMeSport)

Dan wasan bayan Bayern Munich na Kanada Alphonso Davies yana kara jan hankalin Manchester United a baya bayan nan, bayan tattara bayanai kan dan wasan mai shekaru 23 (Sky Germany)

Real Madrid da Chelsea na zawarcin Davies, wanda kwantiraginsa zai kare a bazara mai zuwa. (Express)

Manchester City na sa ido kan dan wasan baya na RB Leipzig Castello Lukeba, mai shekara 21, duk da cewa dan wasan na Faransa ya kulla sabuwar yarjejeniya da kungiyar a kwanan baya. (Fichajes Spanish)

AC Milan ta fara tattaunawa da wakilan dan wasan tsakiyar Netherlands Tijjani Reijnders, mai shekara 26, kan tsawaita kwantiraginsa. (Fabrizio Romano)