Fatana a gama kaka muna cikin Premier League - Amorim

Asalin hoton, Getty Images
Kociyan Manchester United, Ruben Amorim ya ce fatansa shi ne yadda za a kare kakar nan su ci gaba da zama a Premier League.
Ranar Lahadi United ta yi rashin nasara 1-0 a gidan Tottenham a wasan mako na 25 a Premier League, karo na 12 da aka doke ƙungiyar a bana.
Daga wasa takwwas da ta ci da canjaras biyar da rashin nasara 12 shi ne ƙwazo mafi muni tun 1973/13 da ta yi rashin nasara 13 daga nan ta faɗi daga gasar.
Tottenham ta ci ƙwallon ta hannun James Maddison tun a minti na 13 da take leda, kuma hakan aka tashi a fafatawar.
Da wannan sakamakon United tana ta 15 a teburin Premier League da maki 29, bayan da ta ci karawa takwas da canjaras biyar.
Saura gurbi biyu ya rage mata ta shiga cikin ƴan ukun karshe a babbar gasar tamaula ta Ingila ta kakar nan.
United ta buga karawar ba tare da Ahmad Dialo ba, wanda ke taka rawar gani a ƙungiyar, wanda aka ce zai yi jinya mai tsawo.
Ƙungiyar Old Trafford ta fara wasan Tottenham ranar Lahadi ba tare da fitattun ƴan wasa ba, inda Kobbie Mainoo da Manuel Ugarte ke jinya.
Haka kuma masu zaman benci matasa ne guda takwas masu shekara 19 ko kasa da haka da ba su kware ba a buga gasar Premier League.
Wasu ƴan wasan da ba su buga wa United wasan ba sun haɗa da Christian Eriksen da Leny Yoro da kuma Toby Collyer.
Wasa uku da ke gaban United:
Premier League ranar Asabar 22 ga watan Fabrairu
- Everton da Man United
Premier League ranar Laraba 26 ga watan Fabrairu
- Man United da Ipswich
English FA Cup ranar Lahadi 2 ga watan Maris
- Man United da Fulham











