Ƴan Real Madrid da suka doke Atalanta suka ɗauki Uefa Super Cup

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Real Madrid ta doke Atalanta 2-0 ta lashe a Uefa Super Cup ranar Laraba a National Stadium a Warsaw a Poland.

Tuni kuma Carlo Ancelotti ya bayyana ƴan wasan da za su buga karawar ta labulen buɗe gasar kungiyoyin Turai ta 2024/25.

Wannan shi ne karo na tara da Real Madrid ta fafata a European Super Cup, ta kuma ɗauki shida a 2002 da 2014 da 2016 da 2017 da 2022 da kuma a 2024.

Real Madrid ce ta ɗauki Champions League a bara, bayan da ta doke Borussia Dortmund a Wembley, wadda ta lashe kofi na 15 jimilla.

Atalanta ce da lashe Europa League, bayan da ta yi nasara a kan Bayern Leverkusen a kakar da ta wuce.

Wannan shi ne karon farko da Atalanta ta buga kofin, wadda ta kare a mataki na biyar a teburin Serie A da aka kammala a bara.

Ƴan wasan Real Madrid:

Masu tsare raga: Courtois, Lunin and Fran.

Masu tsaron raga: Carvajal, Militão, Alaba, Lucas V., Vallejo, Fran García, Rüdiger, F. Mendy and Jacobo.

Masu buga tsakiya: Bellingham, Camavinga, Valverde, Modrić, Tchouameni, Arda Güler and Ceballos.

Masu cin ƙwallaye: Vini Jr, Mbappé, Rodrygo, Endrick and Brahim.