Halin da ake ciki a wuraren da Isra'ila ke kai hare-hare a kudancin Lebanon

- Marubuci, Lucy Williamson
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Aiko rahoto daga, Southern Lebanon
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Motocin yaƙin rundunar sojin Isra'ila sun riga sun turnuƙe hanyar da muke kai domin shiga Lebanon, inda ƙura ta cika ko'ina. A haka muka tsallake iyakar da aka shata mai nuni da yarjejeniyar tsagaida wuta da aka taɓa ƙullawa tsakanin ƙasashen a shekarun baya.
Ita kanta yarjejeniyar tsagaita wutar ta riga ta tarwatse.
Isra'ila ta ce ta ƙaddamar da harin ƙasa a wannan ɓangaren na Lebanon ne domin abin da ta kira ''Tarwatsa makamai da cibiyoyin Hezbollah''
Kwana goma bayan ƙaddamar da wannan samame, sojojin Isra'ila sun ɗauke mu zuwa wani ƙauye a cikin Lebanon, inda suka ƙwace iko.
An gargaɗe mu cewa ka da mu bayyana sunan ƙauyen, kuma saboda dalilai na aikin soji, an taƙaita zirga-zirgar mu a wajen.
Tankokin yaƙin Isra'ila na ci gaba da ruguden wuta a lokacin da muka isa wajen. Kwamandan rundunar, Kanal Yaniv Malka ya shaida mana cewa a wannan lokacin ba zasu iya bayar da tabbacin cewa sun gama fatattakar mayaƙan Hezbollah daga wajen ba.
Ya yi mana bayanin cewa ɓuraguzan da muke gani sauran tarkace ne na musayar wuta tsakanin mayaƙan Hezbollah da dakarun Isra'ila ƴan kwanaki kaɗan da suka wuce, inda ya ce ɓangarorin biyu sun yi fito na fito da juna.
A iya ganin mu, gidajen da ke gefen hanya ko dai an rushe su ko kuma an rushe wasu sassan su, ga ramin harsashi ta ko ina a jikin katangar gidajen da suka rage ba a ruguza ba.
Ga tankokin yaƙi biyu an girke a tsakiyar filin wasan ƙauyen. Ɓarnar da aka yi a ƙauyen nan, tunatarwa ce da irin halin da ake ciki a Gaza.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Duk da cewa sojojin sun taƙaita zirga-zirgar mu zuwa iyakacin wasu wurare, daga nesa muna iya hangen wasu wurare a ƙauyen waɗanda alamu ke nuna cewa ba a ruguza su ba.
A jikin wani gini a yankin da sojoji suka mamaye, an rubuta saƙon da ke cewa ''Muna son zaman lafiya, ku kuma kun zaɓi yaƙi''
“Mafi yawan ƴan ta'addar sun gudu daga nan,” inji kanar Malka. Ya ƙara da cewa “Amma kafin su gudu sai da suka dasa tarko da bama-bamai a cikin gidajensu. Bayan mun bi gida-gida ne aka muka tabbatar da irin tarkon da suka ɗana. Bamu da zaɓi illa mu rusa gidajen''
Labarin da muka samu kan abin da ya faru a wajen nan, labari ne da sojojin suka bamu kaɗai.
Na tambayi kakakin sojojin ko akwai mata da yara a lokacin da aka ƙaddamar da hare-hare a yankin. Sai ya ce ai an bayar da gargadin neman fararen hula su fice daga yankin kafin samamen.
Sai dai a makon nan ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International ta fitar da rahoton cewa gargaɗin da sojin Isra'ilan suka bayar kafin kutsawa kudancin Lebanon bai wadata ba, kuma ya ket ƴancin kai da ƙasar ke da shi wanda dokar ƙasa da ƙasa ta tabbatar.
An kuma nuna mana wasu makamai da sojojin suka ce sun gano a cikin gidajen fararen hula, ciki harda harsasai da manyan bindigogi harba makaman roka da sabbin na'urorin hangen nesa na zamani.
Ɗaya daga cikin makaman harba roka da aka nuna mana, an riga an fara haɗa shi kamar dai za a harba rokar.

Shi ma babban jami'in runduna ta 91, Roy Russo ya nuna mana wani waje da ya ce ana amfani da shi ne wajen ajiye makmai da kuma haɗa su, inda aka jibe bindigogi da harsasai masu yawa.
“Wannan waje ne da ake tsara yadda za a canza fararen hula zuwa mayaƙan Hezbollah da kuma kitsa yadda za su shiga cikin Isra'ila domin kai hare-hare, wannan ba makamai bane na kare kai.'' In ji Roy Russo.
Isra'ila ta ce wannan ne dalilin ta na ƙaddamar da samame a kudancinb Lebanon, inda ta ce Hezbollah ta jibe makamai kum tana shirin kai harin kan iyaka kmar wanda Hamas ta kai cikin Isra'ila a ranar bakwai ga watan Oktoban bara.
Kafin kutsen da Isra'ila ta yi yankin, sojojin ta sun ce dakarun su na musamman sun shiga yankin kuma sun gano matattarar makamaki da maɓoyar mayaƙan Hezbollah da dama, inda suka tarwatsa mafi yawan su.

Asalin hoton, EPA
Kanal Malka ya nuna mani wasu makamai da ya ce sojojin sun gano a ranar da muka isa ƙauyen. Sun haɗa da ƙananan bama-bamai da kuma makaman zamani masu hangen nesa a cikin dare.
Ya ce makaman da sojojin suka gano a ƙauyen sun ruɓanya waɗanda suka gano a Gaza sau biyu ko sau uku.
“Ba mu da aniyar mamaye wurare a nan. Fatan mu shi ne mu ƙwace makaman da suke da su kuma bayan nan za su dawo su ci gaba da zama ta yadda za su fahimci muhimmancin zaman lafiya'' in ji Kanal Malka.
Bayan yaƙin ƙarshe da aka yi tsakanin Isra'ila da Hezbollah a 2006, Majalisar Dinkin Duniya ta yanke hukuncin cewa dole ne Hezbollah ta janye zuwa arewacin kogin Litani. Kafin wancan lokacin ma an taɓa bayar da umarnin ƙwace makaman su. Duk babu wanda aka aiwatar a ciki.

Asalin hoton, Reuters
Yaƙin 2006 ya fargar da Isra'ila. Ƙungiyar Hezbollah mai samun goyon bayan Iran ta yaƙi sojin Irsa'ila sosai, inda kuma suka yi masu muguwar illa. An shafe shekaru kusan 20 kowanne ɓangare yana taka tsantsan, tare da shirya wa juna, suna jiran dama ta gaba.
Kanal Malka ya yi faɗa a Lebanon a wancan yaƙin. sai dai ya ce yaƙin da ake yi yanzu ''ya banbanta da wancan''
Da aka tambaye shi dalili sai ya ce ''Saboda abin da ya faru ranar bakwai ga watan Oktoba''
Muna cikin magana sai muka ji ƙarar harbe-harbe daga nesa. Ya kalle mu ya ce ''dakaruna ne can ke yaƙi''
Makonni uku kenan da Isra'ila ta tsananta hare-hare a kan Lebanon, ta sama da kuma ta ƙasa a kudancin Lebanon da kuma wasu sassan Beirut.
Lebanon ta ce an kashe mutane fiye da 2,200 kuma an tilastawa wasu fiye da miliyan ɗaya barin muhallin su.
Hezbollah ta fara harba makaman roka zuwa arewacin Isra'ila a ranar takwas ga watan Oktoba, kwana ɗaya bayan Hamas ta ƙaddamar da hari mai muni a kudancin Isra'ila.
Ƙungiyar mai samun goyon bayan Iran tana nuna goyon bayan ta ne ga ƙungiyar Hamas ta Falasɗinu kuma ta ce ba zata daina kai harin ba sai an cimma tsagaita wuta a tsakanin Hamas da Isra'ila.
Isra'ila ta zargi Hezbollah da amfani da fararen hula a matsayin shingen kariya. Kuma wani kwamandan soja ya bayyana samamen da suka kai ta ƙasa a matsayin wani aiki na kare jama'ar Isra'ila daga mamayar Hezbolla.
Hezbollah ta canza salon yaƙin ta tun daga lokacin da Isra'ila ta kutsa Lebanon, inda ta ci gaba da samame a sassan Isra'ilan irin su Metula, wajen da dakarun Isra'ila ta fama da kare yankin daga hare-haren roka.
Mafi yawa dai mutane sun yarda cewa Hezbollah ta ja da baya ne zuwa cikin Lebanon, ba wai guduwa ta yi ba.
Isra'ila ta jibge dakaru da dama a wannan kan iyakr kuma can a gida ana ta kiraye-kirayen ganin dakarun sun mamaye dukkan Gabas ta Tsakiya, ba Lebanon kaɗai ba.
Yayin da yaƙin ya yi ƙamari kuma, sai aka buƙaci mu gaggauta ficewa daga yankin.











