Kashi 66% na masu fama da amosanin jini suna Afirka – WHO

An wallafa

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce fiye da kashi 66 cikin 100 na mutum miliyan 120 a faɗin duniya da ke fama da cutar amosanin jini na nahiyar Afirka.

WHO ta ce kimanin jarirai 1,000 ake haifa kullum tare da cutar a Afirka, abin da ya sa cutar ta zama mafi ƙamari a yankin.

Ta kuma ce fiye da rabin wadannan yaran za su mutu kafin su kai shekara biyar, saboda tsanantar cutar.

Cikin wata sanarwa, ofishin hukumar da ke Afirka ya bayyana cewa mutum 38,403 ne suka mutu sakamakon cutar a 2019 - ƙarin kashi 26 cikin 100 daga shekarar 2000.

Sanarwar ta kuma ce, ministocin lafiya na ƙasashen Afirka, a taron kwamitin WHO na Afirka karo na 72, sun ƙaddamar da yaƙin wayar da kan al'umma da matakan kariya da kuma kula da masu cutar domin rage masu fama da cutar.

Daraktar WHO a Afirka, Dr Matshidiso Moeti, ta ce "akasarin ƙasashen Afirka ba su da isassun kayan aikin da za su samar da kulawar da masu sikila ke buƙata duk da tarin tallafin da ake samu don kariya da gano cutar da wuri da kula da ita. Muna buƙatar mu ƙara faɗakarwa kan cutar da inganta rayuwar masu fama da cutar."

Hukumar ta ƙara da cewa sakamakon rashin tsare-tsaren tantance jarirai da sa ido a sassan nahiyar, akwai ƙarancin alƙaluma da bayanai game da cutar.

Moeti ta ƙara da cewa ya zama dole "mu inganta hanyoyin ba da kulawa da faɗakarwa da kuma tantance jarirai ta hanyar tabbatar da cewa an isar da tsare-tsare zuwa yankuna da cibiyar kual da lafiya a matakin farko."