Yadda Makaɗa suka cashe a Kenya cikin hotunan Afrika

.

Asalin hoton, JEROME FAVRE/EPA

Bayanan hoto, Ranar Talata a ƙasar Senegal makaɗa sun cashe, lokacin gangamin goyon bayan Khalifa Sall ɗan takarar shugabancin ƙasar.
An wallafa
.

Asalin hoton, John Wessels/AFP

Bayanan hoto, Kwanakin baya dubban ƴan Senegal suka yi jerin gwano don neman mahukunta su cika alƙawarin da suka ɗauka na gudanar da zaɓe ba tare da jinkiri ba.
.

Asalin hoton, Khaled Elfiqi/EPA

Bayanan hoto, Ɗaliban Sudan sun hallarci makaranta a birnin Giza da ke ƙasar Masar.
.

Asalin hoton, ESA ALEXANDER/REUTERS

Bayanan hoto, A ranar Alhamis aka kori mutanen da suke zaune a matsugunan wucin gadi a birnin Cape Town da ke ƙasar Afrika ta Kudu.
.

Asalin hoton, ESA ALEXANDER/REUTERS

Bayanan hoto, Wani mai busa yana nishaɗantar da jama'a titin Afrika ta Kudu.
.

Asalin hoton, Guerchom Ndebo/AFP

Bayanan hoto, Yambua Jeannine ƴar shekaru 60, ta na gina matsugunin wucin gadi a ranar Juma'a, bayan tserewa rikicin sojojin Congo da ƴan tawayen M23 waɗanda ake cewa Rwanda na goyon bayansu.
.

Asalin hoton, Moise Kasereka/EPA

Bayanan hoto, Rwanda ta ƙaryata cewar ta na goyon bayan ƙungiyar ƴan tawayen M23 a Gabashin Jamhuriyar Dimukuraɗiyyar Congo, waɗanda suka sa miliyoyin mutane tserewa daga muhallansu.
.

Asalin hoton, Esa Alexander/Reuters

Bayanan hoto, Jama'a sun yi Allah wadai da kasuwancin dabbobi masu rai a duniya, warin da ya ke fitowa daga jirgin dakon dubban shanu ya addabi mutane.
.

Asalin hoton, Luis Tato/AFP

Bayanan hoto, Ranar Alhamis a Kenya jama'a sun yi dandazo don alhini kafin jana'izar Kelvin Kiptum ɗan tseren gudu na duniya.