Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man United ta yi hasarar £113.2m a 2023-24
Manchester United ta sanar da yin hasarar £113.2m a kakar 2023/24 zuwa karshen watan Yuni.
Hakan ya biyo bayan hasarar £28.7m a 2022-23 da kuma £115.5m a 2021-22, kenan ta faɗi kasuwanci a kaka biyar da ya kai fiye da £370m.
Sai dai duk da haka, United na kokarin kada ta yi laifin karya dokar kashe kuɗi daidai samu ta Premier League da kan kwashe maki, idan ƙungiya ta karya ka'ida.
A dokar ta tanadi cewar bai kamata kungiya ta yi hasarar £105m cikin kaka uku ba, inda a bara aka hukuntan Everton da Nottingham Forest, waɗanda aka kwashe masu maki.
A watan Yuli, United ta sanar da cewar za ta rage ma'aikata 250 a wani tsari na kara bunkasa ƙungiyar.
United ta ce tana sa ran samun ƙudi £30m da £35m cikin shekara biyu tun daga 2025.
Ƙungiyar Old Trafford, wadda aka daɗe ana bin bashin £496.52m ta kara da cewar tana sa ran samun £650m, yayin da albashi zai karu da kaso 10 cikin 100 wato £364.7m.
United, wadda za ta kara a Europa League a bana, sakamakon lashe FA Cup a bara, ta ci wasa ɗaya aka doke ta biyu a Premier League ta bana kawo yanzu.
Ƙungiyar ta ɗauki ƴan wasa kan fara kakar nan da ya haɗa da Manuel Ugarte da Joshua Zirkzee da Leny Yoro da Matthijs de Ligt da kuma Noussair Mazraoui.