Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man United na fatan kammala cinikin Lisandro Martinez
Manchester United na ci gaba da tattaunawa da Ajax, kan batun sayen Lisandro Martinez, wanda take fatan kammala cinikin ranar Alhamis.
United ta matsa domin ta dauki dan kwallon mai shekara 24.
An fahimci cewar Martinez, wanda aka alakanta shi da Arsenal ya kagu a kammala cinikin domin ya koma Old Trafford.
Martinez zai zama na biyu da sabon koci, Erik ten Hag zai dauka, bayan Tyrell Malacia da ya koma Old Trafford kan yarjejeniyar kaka hudu daga Feyenoord.
United ba ta tabbatar ko ta kammala daukar Christian Eriksen ba, wanda kwantiraginsa ya kare a Brendford a kakar da ta wuce.
Martinez mai tsaron baya, ya yi wa tawagar Argentina wasa bakwai, wanda ya koma Ajax da taka leda a 2019, ya kuma yi mata wasa 120.