Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man United za ta dauki Dubravka daga Newcastle
Manchester United ta kusan kammala daukar mai tsaron ragar Newcastle United, Martin Dubravka.
Kocin United, Erik ten Hag na fatan daukar dan wasan a matakin ko-ta-kwana ga David de Gea, bayan da ya bayar da aron Dean Henderson ga Nottingham Forest.
Kungiyar Old Trafford ta kasa sayen mai tsaron ragar Eintracht Frankfurt, Kevin Trapp bayan da dan kasar Jamus ya zabi ci gaba da buga Bundesliga maimakon Premier, domin kada ya yi ta dumama benci.
Hakan ne ya sa Ten Hag ya koma zawarcin mai tsaron ragar tawagar Slovakia, Dubravka, mai shekara 33, wanda ya koma Newcastle a 2018.
Koda yake Dubravka ya tsare ragar Newcastle sosai a kakar da ta wuce a Premier League, sai dai yanzu Nick Pope ne ya karbe masa gurbin.
United ta dauki Christian Eriksen da Casemiro da Tyrell Malacia da kuma Lisandro Martinez.
A karshen mako United ta amince za ta dauki dan kwallon Ajax Antony dan kasar Brazil.