Man City na son Cambiso, Borussia Dortmund ta haƙura da Rashford

Andrea Cambiaso

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Andrea Cambiaso
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Chelsea na tunanin zawarcin Alejandro Garnacho, Manchester City na zawarcin Andrea Cambiaso, Borussia Dortmund na auna ƴan wasan baya na Premier biyu na hagu.

Chelsea na tunanin zawarcin ɗan wasan gaban Argentina Alejandro Garnacho, mai shekara 20, bayan Napoli ta kawo ƙarshen zawarcin ɗan wasan na Manchester United. (Sky Sports)

Manchester City na zawarcin ɗan wasan bayan Italiya Andrea Cambiaso, mai shekara 24, amma Juventus za ta buƙaci ta biya fan miliyan 65 (£54.8m) kan ɗan wasan. (Gazzetta dello Sport)

Borussia Dortmund ta janye daga zawarcin ɗan wasan gaban Ingila Marcus Rashford, mai shekara 27, inda biyan ɗan wasan na Manchester United fam 350,000 a duk mako ya zame mata cikas. (Mail)

Ana sa ran ɗan wasan bayan Arsenal da Ukraine Oleksandr Zinchenko, mai shekara 28, zai bar ƙungiyar kafin ƙarshen kakar nan, inda Borussia Dortmund ke sa ido kansa. (Telegraph)

Har ila yau Dortmund tana sa ido kan dan wasan bayan Chelsea da Ingila Ben Chilwell, mai shekara 28. (Sun)

Chelsea ta amince da maganar daukar aron dan wasan tsakiya na Portugal Renato Veiga, mai shekara 21, ga Juventus har karshen kakar wasa ta bana. (Athletic)

Dan wasan baya na Arsenal da Scotland Kieran Tierney, mai shekara 27, yana gab da cimma yarjejeniya kafin ya koma Celtic a matsayin kyauta a karshen kakar wasa ta bana. (Telegraph)

West Ham na zawarcin dan wasan tsakiyar Ingila Dan Neil amma Sunderland ba ta son barin dan wasan mai shekaru 23 a wannan kaka. (Guardian)

Aston Villa na son dauko dan wasan baya na Faransa Loic Bade, mai shekara 24, daga Sevilla, bayan da ta baiwa dan wasan bayan Brazil Diego Carlos, mai shekara 31, damar komawa Fenerbache. (Express Star)

Chelsea na zawarcin dan wasan Hellas Verona da Maroko Reda Belahyane, mai shekara 20, yayin da suke shirin sayar da dan Italiya Cesare Casadei, mai shekara 22. (Gianluca di Marzio)

Dan wasan baya na Jamhuriyar Ireland Andrew Omobamidele, mai shekara 22, yana dab da komawa kulob din Strasbourg na Faransa daga Nottingham Forest. (Athletic)

Wolves ta yi watsi da tayin bude da Millwall ta yi wa dan wasan tsakiyar Ingila Luke Cundle, mai shekara 22, wanda Swansea da Bristol City ke nema. (Express da Tauraro)