Kane zai tsawaita kwantiraginsa da Bayern,Watakil City ta sayar da wasu ƴanwasanta

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Kyaftin ɗin England, Harry Kane, mai shekaru 32, zai sanya hannu kan sabon kwantiragi da Bayern Munich duk da sha'awar da Barcelona ke nunawa a kansa.(Athletic - subscription required), external

Nadin da aka yi wa Enzo Maresca a matsayin kocin Manchester City na iya haifar da gagarumin sauyi a ƙungiyar, inda ake ganin dan wasan Ingila Rico Lewis, mai shekara 21, da dan wasan Netherlands Nathan Aké, mai shekara 31, da kuma dan wasan Sfaniya Nico González, mai shekara 24, da dan wasan Portugal Rúben Dias, mai shekara 29, da kuma dan wasan Brazil Savinho, mai shekara 22, duk na iya kasancewa cikin 'yan wasan da kungiyar za ta sayar.(Mail), external

Manchester City ta shirya kwace dan wasan Newcastle da ƙasar Italiya, Sandro Tonali, mai shekara 26, daga hannun Tottenham, duk da cewa sun riga sun amince da daukar dan wasan Ingila Elliot Anderson mai shekara 23, daga Nottingham Forest.(Marca - in Spanish), external

AC Milan na shirin gabatar da tayin fam miliyan 21.5 kan dan wasan Ingila ,Mason Mount, mai shekara 27, amma Manchester United ba ta son ta sayar da shi.(Mail), external

Hull City na dab da kammala cinikin daukar golan Rangers, Jack Butland, mai shekara 33, yayin da ɗan Croatia Ivor Pandur, mai shekara 26, zai nufi wata hanya ta daban a matsayin ɓangare na yarjejeniyar musayar 'yan wasa domin dawo da dan wasan Ingila gasar Firimiya.(Sun), external

Chelsea ta bayyana ɗan wasan Rayo Vallecano ta Sfaniya Pep Chavarria, mai shekara 28, a matsayin wanda zai maye gurbin Marc Cucurella, ɗan ƙasar Sfaniya mai shekara 27, bayan sayar da shi ga Real Madrid.(Marca - in Spanish), external

Dan wasan Bayern Munich, Michael Olise, ya san cewa kungiyoyi da dama, ciki har da Real Madrid da Paris St-Germain, sun sanya ido kan yadda yake taka leda wa Faransa a gasar cin kofin duniya, inda dan wasan mai shekara 24 zai gana da kungiyar ta Jamus bayan gasar domin tattauna makomarsa.(AS - in Spanish), external

RB Leipzig sun bayyana cewa ɗan wasan Ivory Coast, Yan Diomande, zai ci gaba da kasancewa a ƙungiyar a kakar wasa mai zuwa, duk da rahoton cewa ɗan wasan mai shekaru 19 ya zaɓi Paris St-Germain a matsayin inda zai nufa a gaba. (Florian Plettenberg), external