Yawan sojoji ko kayan aiki: Me Najeriya ta fi buƙata don yaƙar matsalar tsaro?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Cikin mako mai ƙarewa ne rundunar sojin Najeriya ta bayyana aniyar ɗaukar ƙarin dakarun soji fiye da 27,000 a ƙasar a wani yunƙurin da hukumomin ƙasar ke yi na ƙara yawan dakarun rundunar sojinta domin ƙarfafa yaƙi da matsalar tsaron ƙasar.

Matakin na zuwa ne bayan da a baya-bayan nan rundunar sojin ta yaye wasu sabbin kuratan soji fiye da 5,500 da suka fara aiki nan take.

Matsalar ƙarancin wadatattun sojoji da ingantattun kayan aikin dakarun na daga cikin abubuwan da masana ke dangantawa da koma-bayan da Najeriya ke samu wajen magance matsalolin tsaron da take fuskanta.

Masana harkokin tsaro na cewa idan har ƙasar ta za ta mayar da hankali wajen magance waɗannan matsaloli to za a samu sauki a matsalar tsaron da ƙasar ke fama da shi.

Najeriya dai na fama da matsolin tsaro kama daga ƙungiyoyin masu ikirarin jihadi da yan fashin daje da masu garkuwa da mutane da ta yan'aware da rikice-rikicen ƙabilanci da na manoma da makiyaya da sauransu, wani abu da ake ganin na raba hankalin sojojin ƙasar.

Da gaske Najeriya na fukantar ƙarancin soji da kayan aiki?

Masana harkokin tsaro sun tabbatar da cewa Najeriya na fuskantar matsalar ƙarancin jami'an tsaro.

Ƙasar - wadda tafi kowace ƙasa yawan al'umma a nahiyar Afirka - na da yawan sojoji kimanin 280,000 a wacer shafin Global Fire Power Ranking (GFP) mai auka ƙarfin sojin ƙasashen duniya.

Wannan adadi ya ƙunshi dakarun sojin sama da na ƙasa da kuma sojojin ruwa.

Sai dai shafin na GFP ya nuna cewa Najeriya ba ta da sojoji masu jiran ko-ta-kwana.

Dangane da makamai kuwa, shafin na GFP ya ce ƙasar na da jiragen yaƙi 14 da jirage masu saukar ungulu da ke kai hari guda 15 da tankokin yaƙi 182 da sauransu.

A nasa ɓangare Dr Kabiru Adamu shugaban Kamfanin Beacon Security mai nazarin al'amuran tsaro a yankin Saleh ya ce adadin sojojin Najeriya ya kai kimanin 250,000.

''Babu dai tabbacin addadin tun da ka ga kullum wasu na ritaya wasu na mutuwa, wasu kuma suna shiga aiki, amma dai alƙaluman dake bayarwa sun kama tsakanijn 175,000 zuwa 250,000'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Sai dai masanin tsaron ya ce ba yawan adadin sojojin ba ne zai fayyace ko ƙasar na fuskantar ƙarancin sojoji ko akasin haka.

Ya ci gaba da cewa idan ana son yin magana kan wannan sai an duba batutuwa guda uku.

Me ake la'akari da shi don gane ƙarancin soji?

Dr Kabiru Adamu ya ce tsaro na da bangarori uku, da suka ha da da wayan jami'ai da fasaha fda na'urori da haɗuwa ɗan'adam da sabbin fasahohin da a turance ake kira force muliplier.

''To idan ka ɗauki duka waɗannan ɓangarorin, kowannen na da matsalar'', in ji shi.

Masanin tsaron ya ce akwai batun ƙarancin yawan jami'an da kuma matsalar sabbin fasahohi da kayan aiki, da ma makaman da suka buƙata.

''Wani abin da zai ba ka mamaki shi ne yawanci wasu jami'an da ke filin daga sukan yi amfani ne da motoci marasa sulke'', kamar yadda ya ce.

Dr Kabiru Adamu ya ce la'akari da wannan kai tsaye ba za ce Najeriya na fama da karancin jami'an soji ba, sai dai rashin kayan aiki.

''Ai yanzu ma idan ka duba manya ƙasashen duniya abin da suka fi bai wa fifiko a tsaronsu shi ne makamai da kayan aiki, ba wai yawan jami'ai ba'', in ji shi.

Shugaban kamfanin na Beacon Security ya ce duk wanda yake lura da yaƙin Rasha da Ukraine zai tabbatar da haka.

Me Najeriya ta fi buƙata?

Dr Kabiru Adamu ya ce dangane da abin da aka fi buƙata tsakanin abubuwan guda biyu, a iya cewa kayan aiki da fasahohin zamani ne gaba sai kuma yawan sojoji.

''Duk da cewa ana buƙatar yawan sojojin da su yi aiki da waɗannan sabbin fasahohin amma dai kayan aikin da kuma sabbin makaman su ne kan gaba''.

'Yanzu idan ka duba yaƙin Rasha da Ukraine lokacin da aka fara shi, kowa ya yi tsammanin yai ne irn wanda aka aba gani a baya za a yi, amma daga baya kowa ya ga yadda ake yin yaƙin ta hanyar amfani da sabbin fasahohin makamai na zamani'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Abu huɗu ne ke tantance ƙarfin soji

Masanin tsaron ya ce akwai abubuwa guda huɗu mafiya muhimmanci ga kowace ƙasa game da rundunar sojinta, kamar haka:

  • Yawan sojoji da ingancinsu

Wannan ya shafi horo nda tsarin shugabancin da kulawa da rundunar sojin ke samu na abin da ya shari watin gwiwa.

''Wannan shi ne abu na farko dangane da ingancin rundunar soji a kowace ƙasa'', in ji shi.

  • Kimiyya fa fasaha

Wannan ya shafi irin sabbin fasahohin zamani da rundunar sojin ke amfani da iuta wajen aiwatar da ayyukanta.

''Wannan ya ƙunshi fasahohin tattara bayanan sirri ta tantance su, da yadda ake rarraba wa sojojin kayan aikin da suke bukata'', a cewar Dr Kabiru Adamu.

  • Yanayin siyasar Kasar

Wannan ya shafi yadda ƙasa ta fahimci tsaro ta kuma ɗauke shi da muhimmanci, da sanya idanu a ɓangaren tsaron ba tare da yin katsalandan ga buƙatar jami'an tsaron.

"Hakan zai taimaka matuƙa wajen ƙarfin soji da tsaron kowace ƙasa'', in ji shi.