Rukuni na uku na ƴan Najeriya da aka kwashe daga Afrika ta Kudu ya isa Lagos
Rukuni na uku na ‘yan Najeriya da aka kwashe daga kasar Afirka ta Kudu sun isa birnin Lagos, yayin da gwamnati ke ci gaba da kokarin dawo da ‘yan kasar cikin aminci.
Jirgin da ya kawo su ya sauka ne a filin jirgin sama na Murtala Muhammed, inda jami’an gwamnati da na kula da ‘yan gudun hijira suka tarbe su.
Ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta ce waɗanda aka dawo da su sun kai 264 wanda ya haɗa da maza, mata da yara,
Wasu daga cikin wadanda suka iso sun ce sun sha wahala sakamakon rashin tsaro, da kuma takurawa rayuwa a wasu yankunan kasar ta Afirka ta Kudu.
An fara kwaso mutanen ne bayan shafe makonni ana zanga-zangar ƙyamar baƙi a wasu sassan Afirka ta Kudu, da kuma cikar wa’adin ranar 30 ga Yuni da masu zanga-zangar suka bai wa baƙin da ba a wa rijistar zama a ƙasar ba su bar ƙasar. Lamarin ya janyo wasu ‘yan Afirka neman taimakon komawa ƙasashensu.
A baya, kusan mutum 270 aka dawo da su a jirgin farko, yayin da kusan 66 suka biyo baya a rukuni na biyu. Wasu ‘yan Najeriya na cewa zanga-zangar ta bar su cikin damuwa da rashin tabbas kan makomarsu.
Kakakin ma’aikatar, Kimiebi Ebienfa, ya ce gwamnati ta shirya kwaso mutanen ne saboda kare lafiyarsu, yana mai cewa duk wanda ya yi rajista don dawowa shi dole ne a taimaka masa.
Ya kuma bayyana cewa an shirya karin jirage uku a ranakun 3, 6 da 9 ga Yuli ga waɗanda suka yi rajista suna son a dawo da su.
Gwamnati ta shawarci ‘yan Najeriya da ke can da su bi dokokin ƙasar kuma su guji rikici, tana mai lura da yadda lamura ke tafiya.