Hulunan kwalliya da masu yankan alkama a cikin hotunan Afirka

d

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Sanye da wata hula mai ɗaukar hankali, mawaƙiyar Najeriya Tems ta hallara a wani bikin gala da aka shirya da nufin tara kuɗi a birnin New York na Amurka ranar Litinin.
An wallafa
g

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An kuma sanya wata hular ta daban mai ƙirar hawainiya a wani bikin da aka gudanar a Johannesburg na Afirka ta Kudu
g

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Asabar lokacin da wannan matar mai sana'ar kanikanci ke gyaran mota a birnin Nairobi na ƙasar Kenya. Kanikanci sana'a ce da mata ba su fiya yinta ba a nahiyar Afirka.
g

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Juma'a kuma a jihar Sharkia da ke arewacin Masar, wannan ƙaramin yaro na jidon alkama a lokacin da ake yankanta a gona
g

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mata da ƙananan yara a cikin mota lokacin da za a kai su gona domin yankan alkamar, a ranar Juma'a.Masar dai ta ƙara adadin alkamar da take nomawa sakamakon yadda yaƙin Ukraine ya taƙaita samun alkamar a mafi yawan ƙasashen duniya.
g

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ranar Juma'a a Mogadishu babban birnin ƙasar Somaliya, wannan mutumin ɗauke da kifaye a kan babur ɗinsa a lokacin da yake wucewa ta wani titi da ambaliya ruwa ta shafa.
f

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Lahadi an gabatar da wasan kwaikwayo a gidan wasa na 'amphitheatre' da ke birnin El Jem a ƙasar Tunisiya, ciki har da wasan kwaikwayon da ke nuna al'adun daular Romawa.
v

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Lahadi wani fitaccen tsohon sojan Senegal da ake yi wa laƙabi da "Senegalese Sniper" ya gana da shugaban ƙasar Macky Sall . Tsohon sojan na daga cikin sojoji tara da suka yi wa Faransa yaƙi tsakanin shekarun 1940 zuwa 1960 a ƙasashen Aljeriya da Vietnam.
g

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A lokacin da suke tsakanin shekarun 85 zuwa 96, an tilasta musu zama a Faransa domin karɓar kuɗin fansho na tsufa, amma a yanzu sun koma gida.