Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Modric ya buga wa Real Madrid wasa na 350 a La Liga
Ranar Lahadi Real Madrid ta doke Celta Vigo da cin 4-0 a wasan mako na 28 a gasar La Liga.
Real Madrid ta ci gaba da zama ta daya a kan teburi da maki 69, sai Girona ta biyu da maki 62 da kuma Barcelona mai rike da kofin bara da maki 61 a mataki na uku.
Luca Modric ya buga karawar a Santiago Bernabeu kuma wasa na 350 da ya yi kenan a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Dan kasar Croatia shi ne kan gaba a yawan buga wasanni a Real Madrid a yanzu haka, wanda aka ci karawa 236 da shi a fili da canjaras 62 da rashin nasara 52.
Modric ya lashe kofin La Liga uku a kungiyar a kakar (2016-17 da 2019-20 da kuma 2021-22) da cin kwallo 28 kawo yanzu.
Ya fara buga wasan La Liga cikin Satumbar 2012 a karawa da Granada a Bernabeu, kuma a kakar 2020/21 ya buga fafatawa 35 mafi yawa da ya yi kenan.
Ya fuskanci Atletico Madrid da yawa fiye da kowacce kungiya a La Liga sau 23.