Mbappe ne kan gaba a takarar takalmin zinare a Gasar Kofin Duniya

Asalin hoton, Getty Images
Ranar Talata za a ci gaba da wasannin daf da na kusa da na karshe a Qasar Cin Kofin Duniya a Qatar, bayan da aka kammala zagaye Quarter finals.
Ranar Talata za a kara tsakanin Argentina da Croatia, sannan a fafata tsakanin Faransa da Morooco ranar Laraba.
Kawo yanzu an ci kwallo 158 a babbar Gasar tamaula ta duniya da Qatar ke karbar bakunci, inda Kyalin Mbappe ke kan gaba mai biyar a raga kawo yanzu.
Cikin masu takarar takalmin zinare a Qatar, wato kyautar da ake bai wa wanda ke kan gaba a cin kwallaye har da Lionel Messi na Argentina da Olivier Giroud na Faransa.
Messi mai taka leda a PSG da kuma Giroud mai wasa a AC Milan kowanne ya ci hurhudu.
Mbappe ya fara cin kwallo a Qatar a minti na 68 a karawar da Faransa ta ci Australia 4-1 ranar 22 ga watan watan Nuwamba.
Daga nan ya ci biyu a fafatawar da Faransa ta doke Denmark 2-1 ranar 26 ga watan Nuwamba.
Haka kuma dan kwallon PSG ya kara zura biyu a raga a wasan da Faransa ta ci Poland 3-1 ranar 4 ga watan Disamba.
Ranar 18 ga watan Disamba za a kammala Gasar Cin Kofin Duniya ta 22 da Fifa ke gudanarwa.
Jerin 'yan wasan da ke takarar lashe takalmin zinare a Qatar
- Kylian Mbappe 5
- Lionel Messi 4
- Olivier Giroud 4
- Enner Valencia 3
- Richarlison 3
- Goncalo Ramos 3
- Bukayo Saka 3
- Cody Gakpo 3
- Alvaro Morata 3
- Marcus Rashford 3











