Sabuwar dambarwa ta kunno kai a jam’iyyar PDP a jihar Katsina

Jam'iyyar PDP

Asalin hoton, OTHER

An wallafa

Sabuwar dambarwar siyasa ta kunno kai a babbar jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Katsina da ke Najeriya, wanda wasu ke ganin yana iya kawo mata cikas a zaben 2023.

Zuwa yanzu dai ana iya cewa jam’iyyar ta PDP ta rabu gida biyu, bayan da ɓangaren Salisu Yusuf Majigiri ke cewa har yanzu shi ne shugaban PDP na Katsina, jim kaɗan bayan rantsar da Alhaji Lawal Magaji Ɗan-ɓaci a kan wannan muƙami.

 Honorabul Bashir Tanimun Garba, tsohon sakataren jam’iyyar PDP a yankin arewa maso yammacin Najeriya, daya daga cikin ‘yan bangaren Salisu Yusuf Majigiri, ya shaida wa BBC cewa, an yi nadin sabon shugaban jam’iyyar ba bisa ka’ida ba.

 Ya ce bangaren dan takarar gwamnan jihar a jam’iyyar ta PDP, Yakubu Lado, ne suka yi taro ya fada wa jama’a cewa wai Salisu Yusuf Majigiri ya yi murabus, to wannan hakan ba gaskiya ba ne.

 Bashir Tanimun Garba ya ce “Ba murabus ya yi ba riko ya yi saboda zababbe ne, don ya ci zaben fid da gwani ba wai ya ci babban zabe ba ne, rantsuwa guda biyu aka haramta, amma ba haramta cewa mutum ya tsaya takarar wata kujera ba don yana zababbe.”

Tsohon sakataren jam’iyar PDP a yankin arewa maso yammacin Najeriya, ya ce su abin da suka sani Salisu Yusuf Majigiri, shi ne har yanzu shugaban jam’iya na PDP a Katsina.

“ Abin da kundin tsarin mulkin kasa ya haramta shi ne kada mutum ya yi rantsuwa sau biyu, don haka ba bu dalilin cewa ya yi murabus” in ji shi.

Bashir Tanimun Garba, ya ce,” Abin da ya kawo wannan abu shi ne saboda Salisu Yusuf Majigiri, ya tsaya takara tare da dan takarar gwamna na yanzu Yakubu Lado, kuma shi ne ya zo masa na biyu, sannan koda aka ce yazo na biyu a zaben fidda gwanin bai yi wata gardama ba take ya amince da sakamakon zaben, amma duk da haka aka tsangwame shi.”

Ya ce, “ A yau idan har mun samu takardar da Salisu Yusuf Majigiri shugaban jam’iyar ta PDP reshen jihar Katsina ya yi murabus, to ko shakka ba bu zamu amsa.” In ji Bashir Tanimu Garba.

Ya ce, su abin da suka sani Salisu Yusuf Majigir ne shugaban jam’iyar, don haka a mai do shi a matsayinsa da kowa ya sani.

 Ko da BBC ta tuntubi bangaren sabon shugaban jam;iyar ta PDP a katsinan, Alhaji Lawal Magaji Ɗan -ɓaci, sai bangaren ya ce ba bu abin da zai ce kan wannan lamari.

Sabuwar dambarwar dai ta bullo ne a daidai lokacin da jam’iyun siyasa a Najeriya ke kokarin hada kan ‘ya’yansu don tunkarar babban zaben 2023.