Onana ya bar sansanin Kamaru ya gama buga kofin duniya a Qatar

Onana

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Andre Onana ya bar sansanin Kamaru ya gama buga mata Gasar Kofin Duniya, bayan da hukumar kwallon kasar ta dakatar da shi.

Wata majiya da take kusa da dan wasan ta sanar da BBC cewar Onana ya bar otal din tawagar zuwa filin jirgin sama, domin komawa Kamaru.

Hukumar kwallon kafar Kamaru ta dakatar da golan, bayan rashin jituwa tsakanin Rigobert Song da Onana, wanda ya ce kada a saka shi a wasa na biyu a Qatar.

Mai shekara 26 da ke taka leda a Inter Milan an maye gurbinsa da Devis Epassy a wasan ranar Litinin da suka tashi 3-3 da Serbia, kuma Onana baya cikin 'yan zaman benci.

Ranar Litinin hukumar kwallon kafa ta Kamaru ta fitar da wata sanarwar cewar ta dakatar da Onana kan halin rashin da'a daya nuna.

Onana, wanda ya buga wa Kamaru wasa 34 ya yi wa kasar dukkan karawa a shekarar nan, kafin a ajiye shi a wasan Serbia a Qatar

Shugaban hukumar kwallon kafar Kamaru, Samuel Eto'o ya ce suna goyon bayan kociya Song mai shekara 46, kan hukuncin da ya dauka kan ajiye golan tun farko.

Tun farko an samu hatsaniya kan cewar Song baya kaunar Onana da yake barin da'ira ta 18 a karo da yawa.

Cikin kwallo 61 da Onana ya taba a ranar Alhamis da Switzerland ta yi nasara da ci 1-0, guda 26 Onana ya taba a wajen da'ira ta 18 ne.