Southampton ta kammala ɗaukar Brereton Diaz daga Villareal

Asalin hoton, Getty Images
Southampton ta kammala ɗaukar ɗan wasa, Ben Brereton Diaz daga Villarreal kan kusan fam miliyan 7.
Ɗan wasan tawagar Chile ya rattaba hannu kan kwantiragin kaka hudu a St Mary, bayan wata 12 da ya yi a ƙungiyar da ke buga babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Brereton Diaz ya koma La Liga, bayan kwantiraginsa ya kare a Blackburn, sai dai bai ci ƙwallo ba a wasa 20 da ya buga.
Ɗan wasan ya shafe rabin kakar bara a matsayin aro a Sheffield United, inda ya zura kwallo shida a wasa14 a gasar Premier.
Southampton ta kasance tana neman sabon ɗan wasan gaba, bayan Che Adams ya koma Torino a wannan watan, bayan ya ki amincewa da sabon tayin kwantiragi da Southampton ta yi masa.
Brereton Diaz ya fara taka leda a Nottingham Forest daga nan ya shafe kaka biyar a Blackburn Rovers, inda ya zura kwallo 47 a wasa 177.
Ya koma buga wa tawagar Chile tamaula, bayan da ya taka leda a tawagar Ingila ta matasa, wadda ya buga wa tamaula a 2021.
Mai shekara 25 ya buga wa Chile wasa uku a Copa America, gasar da Argentina ta lashe a bana a Amurka.
Ya zama na baya bayan nan da Southampton ta ɗauka a bana da ya hada da Adam Lallana, Taylor Harwood-Bellis, Charlie Taylor, Ronnie Edwards, Nathan Wood, Yukinari Sugawara da Flynn Downes.
Southampton tana ta shirye-shiryen yadda za ta taka rawar gani a Premier League, bayan da ta samu gurbin shiga wasannin a bara daga Championship.











