Abin da hade yankunan Ukraine da Rasha ta yi yake nufi

An wallafa

Ta yaya Rasha za ta hade yankuna hudu da ba ta karbe ikonsu baki daya ba, yayin da take tsaka da tafka yaki?

Ranar Juma'ar nan ne Vladimir Putin ya sanya hannu a kan wata takarda da ta hade wasu yankuna hudu da ta mamaye bayan ya ayyana cewa kasarsa ba za ta taba rabuwa da su ba kuma za ta kare su ko ta halin kaka.

Me ya sa sai yanzu ya dauki matakin?

Shugaban Rasha yana tsaka mai wuya. Yakin da ya kwashe wata bakwai yana yi ba ya samun galaba a yayin da Ukraine take kai wa dakarunsa hare-haren rayuwar gayya abin da ya ci karo da shirinsa na farko na mallakar yankuna biyu na gabashin kasar wato Luhansk da Donetsk.

Ya yi kuri'ar raba-gardama a dukkanin yankuna hudu da Rasha ta mamaye lamarin da ya janyo masa suka daga kasashen duniya wadanda suka bayyana kuri'ar a matsayin wala-wala domin kuwa a wasu lokutan ana sa wa sojoji su je gida-gida suna tattaro masu kada kuri'a.

Idan ya hade wadannan yankuna tare da Zaporizhzhia da Kherson da ke kudancin kasar zai samu damar tura sabbin dakarun da aka dauka fagen yaki kuma zai yi wa kasashen Yamma barazanar kada su kuskura su bar makamansu su nufi yankuna da ya ce na Rasha ne.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya yi alla-wadai da matakin na Rasha a matsayin mai hatsarin ta'azzara halin da ake ciki: "Duk wani mataki na hade yakunan Donetsk, Luhansk, Kherson da Zaporizhzhia na kasar Ukraine bai da halasci kuma ya kamata a yi tur da shi.

Matakin ba zai taba yin daidai da dokokin kasashen duniya ba; ya saba da dukkan muradun kasashen duniya; kazalika ya ci karo da ginshikan da aka kafa Majalisar Dinkin Duniya.

Kamar abin da ya faru ga Crimea?

Matakin ya yi kama da abin da Shugaba Putin ya yi a watan Maris na 2014, inda ya kwace yankin Crimea daga Ukraine, sannan ya yi kira a gudanar da kuri’ar raba-gardama wadda kasashen duniya suka yi tur da ita kuma ya kwace yankin ta irin wannan hanya ta tsarin mulki har ta kai ga majalisar dokokin Rasha ta kada kuri’ar goyon baya.

Rasha ta kwace Crimea ba tare da zubar da jini sosai kuma ta karbe yankin baki daya.

Ta wata fuskar a iya cewa dukkan yankunan hudu da Rasha ta hade har yanzu suna hannun Ukraine a mataki na kwarya-kwarya.

Yankunan su ne kashi 15 na baki daya kasar Ukraine.

Yankunan biyu da ke gabashin kasar na hannun 'yan tawayen da Rasha ke mara wa baya tun 2014, sai dai kashi 60 na Donetsk ne kawai Rasha za ta iya tutiyar kwacewa bayan ta kwashe wata shida tana yaki, ita kuwa Luhansk tana tsakiyar farmakin da Ukraine ke kai wa.

Nan da awanni masu zuwa dakarun Rasha za su iya shan kashi a garin Lyman da ke da matukar muhimmanci.

Babban birnin lardin Zaporizhzhia yana hannun dakarun Ukraine sosai, ko da yake makamai masu linzami na Rasha ka iya kai wa gare shi, kuma dakarun Ukraine ba su da nisa da birnin Kherson.

Ta yaya za ka hade yankuna hudu da ba ka da iko a kansu? Ko mece ce ansar wannan tambayar, shugaban Rasha yana gaggawar yin haka, inda ya sanar da yin kuri'ar raba-gardama ba tare da bayar da isasshen lokaci ba.

A yayin da yake jawabi na hade yankunan, Shugaba Putin ya yi kira ga Ukraine ta tsagaita wuta kana ta dawo kan teburin tattaunawa, amma ya bayyana karara cewa yankunan ba za su sake komawa hannun Ukraine ba.

Kakakin fadar Kremlin Dmitry Peskov ya fada ranar Juma'a cewa duk wani hari da za a kai a yankunan da aka hade zai zama tamkar tsokanar fada.

Mene ne zai sauya?

Abin da zai sauya ba a fayyace yake ba. Shi kansa Mr Peskov bai iya bayyana inda Rasha za ta shata sabbin iyakokinta ba a yankunan kudancin Ukraine.

Amma ya ce Rasha za ta dauki dukkan lardin Donetsk a matsayin kasarta.

Su kuwa yankunan da ba ta mamaye ba, ya ce za a sama musu 'yanci.

"Hakan zai zama wata hanya ta karkatar da hankalin 'yan kasar Rasha da ma kasar ita kanta," a cewar Paul Stronski na Carnegie Endowment for International Peace, wanda ya yi amannar cewa abin da zai sauya ba shi da yawa a zahiri.

Wanne martani Ukraine za ta mayar?

Shugaba Volodymyr Zelensky yana ta gagganawa da manyan hafsoshin tsaro domin su yanke shawara kan martanin da za su mayar, sai dai ya riga ya bayyana karara cewa hade yankunan ba zai bai wa Kremlin abin da take burin samu ba.

Wanne hatsari matakin ke da shi?

Babu wanda ya san abin da ke zuciyar gwamnatin Rasha, amma dai a bayyane take cewa tana so kasashen Yamma da Ukraine su kalli kai hari kan yankunan da aka hade a matsayin kai hari a kan Rasha ita kanta.

Tuni Shugaba Putin ya yi barazanar yin amfani da duk wata dama da yake da ita domin kare yankunan Rasha, ciki har da amfani da makamin nukiliya.