Matsalar amfani da 'kazaman kudade' a siyasar India

An wallafa

An samar da tsarin takardun lamunin kudin zabe ne da zummar tsarkake hanyoyin da jam'iyyun siyasa ke samun kudadensu a India. Amma ana kalubalantar tsarin a Kotun Kolin kasar inda wasu ke bayyana shi a matsayin "jirkita dimokuradiyya".

Kotun Kolin kasar na shirin komawa aiki - bayana shekara biyu - domin sauraren korafe-korafe game da takardun lamuninn kudi na zabe, wadanda kafofi ne na bayar da gudunmawa ga jam'iyyun siyasa ba tare da kudin ruwa ba.

An kaddamar da shirin ne a 2018, wanda aka yi masa wa'adi kuma ba a karbar kudin ruwa a kansa kan takardun kudi da suka soma daga - rupee 1,000 zuwa miliyan 10 ($12.50 to $125,000) - sannan ana iya sayensu a bankunan gwamnati a wasu lokuta da aka ware.

An amince 'yan kasar da kuma kamfanoni su sayi takardun lamunin kudin na zabe sannan su bayar da su kyauta ga jam'iyyun siyasa, wadanda za su sauya su zuwa tsabar kudi cikin kwana 15.

Jam'iyyun da aka yi wa rajista ne kadai da kuma suka samu abin da bi gaza kashi daya na kuri'un a zaben da ya gabata na kujerun majalisar dokokin tarayya ko jihohi suka cancanci samun wadannan takardun lamuni.

An sayar da takardun lamunin kudin zabe na kimanin $1.15bn a lokuta 19 kawo yanzu, a cewar gwamnatin kasar. Da alama jam'iyyar Bharatiya Janata Party (BJP) ta Firaiminista Narendra Modi ce ta fi cin moriyar wadanda suka ba ta kyautar takardun lamunin zaben, inda ta samu daya bisa uku na takardun lamunin a kakar zabe ta 2019-20, idan aka kwatanta da babbar jam'iyyar adawa ta Congress wadda ta samu kashi tara na takardun lamunin.

Manyan jam'iyyu bakwai na kasar sun samun kashi 62 na kudaden shigarsu daga gudunmawar da suka samu ta hanyar takardun lamunin kudin zabe a wanna shekarar, a cewar hukumar kungiyar da ke sanya ido kan zabe ta Association for Democratic Reforms (ADR).

An fito a tsarin takardun lamunin kudin zaben ne da zummar magance matsalar kudaden haramun sannan a samar da hanyar samun kudaden zabe ba tare da kumbiya-kumbiya ba. Sun ce na yin batun takardun lamunin ne cikin sirri.

Babu wasu ajiyayyun bayanai game da wadanda ke sayen takardun lamunin da kuma wadanda suka bai wa gudunmawarsu. Hakan ya sa takardun suka kasance matsala a tsarin "mulki" a yayin da masu biyan haraji ke cikin duhu game da ainihin inda ake samun wadannan kudaden gudunmawa, a cewar ADR.

Kazalika, 'yan hamayya sun ce ba dukkan batun takardun lamunin ne yake cikin sirri ba: tun da bankunan gwamnati suna da sunayen mutanen da suka bayar da gudunmawa da kuma wadanda suka karba, cikin sauki gwamnati za ta samu bayanansu sannan su yi "amfani" da su wajen samun tagomashi kan masu bayar da gudunmawar.

"Takardun lamunin kudin suna taimaka wa jam'iyya mai mulki," a cewar Jagdeep Chhokar, daya daga cikin wadanda suka kafa ADR.

Lokacin da aka kaddamar da takardun lamunin a karon farko a 2017, hukumar zaben India ta ce za su yi "katsalandan" kan tsarin zaben kasar.

Babban bankin kasar da ma'aikatar shari'a da kuma 'yan majalisar dokoki da dama sun tsoma baki cikin batun, suna masu cewa takardun lamunin kudin zaben ba za su hana zuba kazaman kudade a harkokin siyasar kasar ba. (Shekara guda bayan wadannan kalamai hukumar zzben ta yi amai ta lashe inda ta goyi bayan takardun lamunin.) Kazalika kotu ta jinkirta yanke hukunci kan batun.

"Gwamnati ta halasta kumbiya-kumbiya ta hanyar takardun lamunin kudin zabe," a cewar Milan Vaishnav na Gidauniyar Carnegie Endowment for International Peace, da ke da hedikwata a birnin Washington.

"Masu bayar da gudunmawa suna iya bayar da gudunmawa komai girmanta ga jam'iyyu kuma ba tilas ba ne dukkan bangarorin biyu su bayyana hakikanin abin da ya faru. Idan har ana tallata hakan a matsayin 'keke-da-keke', gaskiya wannan ba haka ba ne," in ji shi.

Babu wanda yake kokwanton cewa India na bukatar inganga tsarin samun kudin harkokin siyasarta. Zabuka na da matukar tsada kuma daidaikun mutane da kamfanoni ne suke bayar da gagarumar gudunmawar kudin harkokin siyasa - An yi kiyasin cewa zaben 2019 ya lakume fiye da $7bn, mafi tsada a duniya bayan zaben da ake yi a Amurka.

Girman adadin masu kada kuri'a - fiye da mutum miliyan 900 ne suka cancanci kada kuri'a a zabukan 2019, daga kasa da mutum 400,000 a 1952 - na nufin 'yan takara na kashe makudan kudade wajen yakin neman zabe.

Kazalika matakai uku da ake gudanar da zabe a kansu - kauyuka, jihohi da kuma tarayya - sun sa ana yin zabe kashi-kashi. Haka kuma ana yin fafatawa mai zafi a lokutan zabuka.

Jam'iyyun siyasa suna mika bayanai game da yadda suke kashe kudadensu ga hukumar zabe a duk shekara. Kudaden da suka fito daga "kafofin da ba a sansu ba" - mutane da dama sun ce wadannan kafofi sun hada da takardun lamunin kudin zabe - wadanda suka kai kashi 70 na dukkan kudaden, a cewar ADR. Mr Vaishnav ya ce takardun lamunin "sun sanya ana fada kan yin garambawul game da kudin yakin neman zabe da aka kwashe shekaru ana amfani da su".

A Clearly, India's road to political finance reform is long - and tortuous.