Ƴan Real da aka gayyata tawagoginsu buga wasanni

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

An gayyaci ƴan wasan Real Madrid da yawa, domin buga wa tawagoginsu wasanni tun daga cikin makon nan.

Daga ciki sun haɗa da Modric da Rüdiger da Camavinga da Tchouameni da Bellingham da Arda Güler da Rodrygo da Endrick da kuma Valverde.

Za a buga Nations League a nahiyar Turai, yayin da Brazil da Uruguay za su buga wasan neman shiga gasar kofin duniya na 2026.

Wasannin da ƴan Real Madrid za su buga:

  • Ingila da Girka Alhamis 10 ga watan Oktoba
  • Finland da Ingila Lahadi 13 ga watan Oktoba

Bellingham zai buga wa Ingila wasa biyun da za ta yi a Nations League, inda za ta fara na farko a Wembley, sannan ta je Helsinki ta kara da Finland.

  • Israel da Faransa Alhamis 10 ga watan Oktoba
  • Belgium da Faransa Litinin 14 ga watan Oktoba

Camavinga da Tchouameni za su buga wa Faransa Nations League a karawar farko a Bozsik Arena a Budapest, sai wasa na biyu a King Baudouin Stadium a Brussels da Belgium.

  • Chile da Brazil Juma'a 11 ga watan Oktoba
  • Brazil da Peru Laraba 16 ga watan Oktoba

Rodrygo da Endrick za su buga wa Brazil wasa biyu a neman shiga gasar kofin duniya. Za ta fara da zuwa Chile, sannan ta fuskanci Peru a gida.

  • Bosnia da Jamus Juma'a 11 ga watan Oktoba
  • Jamus da Netherlands Litinin 14 ga watan Oktoba

Rüdiger zai yiwa Jamus Nations League da za ta je Bosnia, sannan ta yi wa Netherlands masauki.

  • Turkiya da Montenegro Juma'a 11 ga watan Oktoba
  • Iceland da Turkiya Litinin 14 ga watan Oktoba

Arda Güler zai wakilci Turkiya a Nations League da za ta fafata da Montenegro a gida, sannan ta je Iceland a wasa na biyu.

  • Peru da Uruguay Asabar 12 ga watan Oktoba
  • Uruguay da Ecuador Laraba 16 ga watan Oktoba

Shi kuwa Valverde zai buga wa Uruguay wasan neman shiga gasar kofin duniya, inda za su fara zuwa gidan Peru, sannan ta kara da Ecuador a gida.

  • Croatia da Scotland Asabar 12 ga watan Oktoba
  • Poland da Croatia (Talata 15 ga watan Oktoba

Ƙyaftin ɗin Real Madrid zai buga Nations League a wasa da Scotland a Maksimir stadium a Zagreb, sannan ta je Poland.