Champions League: Kovacs ne zai busa wasan Real da Man City

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar ƙwallon kafa ta Turai, UEFA ta bayyana Istvan Kovacs a matsayin wanda zai yi rafli a wasan Real Madrid da Manchester City ranar Laraba.
Ƙungiyar da ke buga Premier League za ta je Sifaniya, domin buga wasa na biyu zagayen cike gurbi a Champions League.
Ranar Talata 11 ga watan Fabriru Real Madrid ta je ta ci Manchester City 3-2 a wasan farko na cike gurbi a gasar ta zakarun Turai a Etihad.
Erling Haaland ne ya ci wa City ƙwallo biyun har da ɗaya a bugun fenariti, ita kuwa Real ta zura ukun ta hannun Kylian Mbappe da Brahim Diaz da kuma Jude Bellingham.
Karon farko da Real ta yi nasara a Etihad a wasa bakwai da ta je filin, inda a wasa 13 da suka fafata a tsakaninsu Real da City kowacce ta yi nasara huɗu da canjaras biyar.
Kovacs ɗan kasar Romania zai busa wasan Real Madrid a gasar zakarun Turai karo na huɗu a tarihi.
Kuma karo na biyu da zai yi alkalancin karawa tsakanin Real da City, shi ne rafli a lokacin da City ta ci Real 4-3 a daf da karshe a Champions League a 2021/22.
Wasa uku da Kovacs ya busa wa Real Madrid:
- Real Madrid 5-2 Borussia Dortmund Champions League league 2024/25.
- Liverpool 2-5 Real Madrid Champions League 2022/23.
- Manchester City 4-3 Real Madrid Champions League 2021/22.











