Su wane ne sabbin shugabannin hukumomin leƙen asiri na Najeriya?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

A ranar Litinin ne shugaban Najeriya Bola Tinubu ya naɗa sabon shugaban Hukumar tattara bayanan sirri ta Najeriya (NIA) da kuma shugaban Hukumar ƴansandan ciki ta ƙasar (DSS).

Mohammed Mohammed shi ne wanda shugaban ƙasar ya naɗa a matsayin sabon shugaban Hukumar tattara bayanan sirri ta ƙasar.

Sai kuma Adeola Oluwatosin Ajayi wanda shi kuma aka naɗa a matsayin shugaban Rundunar ƴansandan farin kaya.

Naɗin nasu na zuwa ne bayan saukar tsoffin shugabannin hukumomin guda biyu, bagatatan.

Adeola Ajayi shi ne ya maye gurbin Yusuf Magaji Bichi, wanda tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya naɗa a shekarar 2018.

Shi kuma Mohammed Mohammed ya maye gurbin Ahmed Abubukar, wanda ya ajiye muƙaminsa a cikin ƙarshen makon da ya gabata.

A ranar Asabar ne tsohon shugaban Hukumar tattara bayanan sirrin ta Najeriya ya miƙa takardar ajiye aiki bayan wata ganawa da ya yi da shugaban ƙasa Bola Tinubu.

Ahmed Abubakar dai bai bayyana dalilan da suka sanya ya ajiye aikin nasa ba.

Sai dai ba kamar shugaban na NIA ba, tsohon shugaban rundunar ƴansandan farin kaya ta DSS, Yusuf Magaji Bichi, bai sanar da ajiye aikin nasa ba, sai dai aka ga sanarwar naɗa sabon shugaban rundunar a ranar Litinin

Wane ne Mohammed Mohammed?

Mohammed ya fara aiki ne da hukumar tattara bayanan sirri ta Najeriya a shekarar 1995, kuma tun daga wancan lokaci ya taka matakai da dama.

Ya riƙe muƙamai da dama har zuwa muƙamin darakta da kuma muƙamin da ya riƙe a baya na shugaban tawagar Najeriya a Libiya.

Mutumin wanda ya kammala karatunsa a 1990 a Jami’ar Bayero da ke Kano, ya yi aiki a ƙasashen Koriya ta Arewa da Pakistan da Sudan da kuma fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Wane ne Adeola Oluwatosin Ajayi?

Adeola Oluwatosin Ajayi ya riƙe muƙamai da dama har zuwa muƙamin mataimakin shugaban DSS kafin naɗa shi kan wannan muƙami.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, hukumar DSS ta bayyana Ajayi a matsayin jami’i mai ƙwazo.

Ya fara aiki ne da hukumar a shekarar 1990.

Sanarwar ta ƙara da cewa “Sabon shugaban hukumar ya samu horo a ɓangarori daban-daban da suka shafi gudanarwa da tsaro da shugabanci da sauran su, a ciki da wajen Najeriya.”

Ya kuma shugabanci hukumar a jihohi da dama na Najeriya, kamar Rivers da Bauchi da Enugu da Bayelsa da kuma Kogi.

Shugaban Tinubu ya buƙaci sabbin shugabannin biyu su yi aiki cikin ƙwarewa domin inganta lamarin tsaro na ƙasar.

Aikin da ke gaban sabbin jami'an

Mutanen biyu dai sun karɓi ragamar shugabancin waɗannan muhimman hukumomi biyu ne yayin da Najeriya ke ci gaba da fuskantar matsaloli na tsaro.

Ana dai zargin hukumomin tsaro a Najeriyar da rashin kataɓus a ɓangaren tattara bayanan sirri da za su iya kawo ƙarshen matsalolin tsaron da ƙasar ke fama da su.

Har yanzu Najeriya na fama da hare-haren mayaƙan Boko Haram jefi-jefi a arewa maso gabashin ƙasar.

Haka nan yankin arewa maso yammacin ƙasar na fama da matsalar hare-haren ƴan bindiga, waɗanda a makon da ya gabata suka hallaka wani basarake a jihar Sokoto bayan kwashe fiye da mako uku suna garkuwa da shi.

Lamarin da ya janyo allah-wadai da nuna damuwa kan yadda ƴan bindigar ke ci gaba da cin karenmsu babu babbaka duk da ƙoƙarin da gwamnati ta ce tana yi.

Wasu ƴan Najeriya na cewa suna mamakin yadda ake tattaunawa da irin waɗannan masu satar mutane a wayar tarho ana yarjejeniya kan kuɗin fansa, amma hukumomin tsaro sun kasa ɗaukar matakin samun su inda suke domin murƙushe su.

Hukumar NIA a Najeriya ita ce wadda doka ta ɗora wa alhakin tattara bayanan sirri daga ƙasashen duniya tare kuma da yaƙi da ayyukan masu leƙen asiri a cikin ƙasar.

Ita kuwa DSS ɗaya ce daga cikin hukumomin tsaro na ƙasar waɗanda ke yaƙi da ayyukan da za su iya yin barazana ga zaman lafiya a cikin ƙasar.

Hukumar na cikin na gaba-gaba wajen fitar da sanarwar gargaɗi kan ayyukan da suka shafi tayar da hargitsi ko zanga-zanga.

Ko a ƙarshen watan Yuli, hukumar ta gargaɗi wasu matasa da suka shirya zanga-zangar nuna fushi kan matsin rayuwa, game da cewa akwai waɗanda za su ƙwace zanga-zangar domin tayar da hargitsi.