Hummels zai yi ritaya daga taka leda

Matts Humels

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ɗan wasan tawagar Jamus, Mats Hummels, wanda ya taɓa lashe kofin duniya, zai yi ritaya daga taka leda a karshen kakar bana.

Yarjejeniyar ɗan wasan mai shekara 36 za ta kare a karshen watan Yuni a Roma, ya sanar a kafarsa ta sada zumunta zai hakura da murza leda a karshen kakar nan.

Hummels yana cikin tawagar Jamus wadda ta lashe kofin duniya a 2014, wadda ya buga wa wasa 78 tsakanin 2010 zuwa 2023 da cin ƙwallo biyar.

Ya fara tamaula tun daga matashi a Bayern Munich da yi mata wasa a karon farko a a Mayun 2007 yana da shekara 18 da haihuwa.

Ya koma Borussia Dortmund a Janairun 2008 a matakin aro, daga nan ya zama kashin bayan ƙungiyar har da lashe kofin Bundesliga biyu karkashin Jurgen Klopp.

Hummels ya sake komawa Bayern a 2016, wanda ya lashe karin kofi uku daga nan ya sake komawa Dortmund a karo na biyu da buga kaka uku a ƙungiyar.

Mai tsaron bayan, ya buga wasan karshe karo biyu a Dortmund a Champions League a 2013 da kuma 2024, amma bai samu damar lashe kofin zakarun Turan ba.

Hummels ya yi wa Dortmund karawa 508, sannan ya buga wasa 118 a Bayern Munich.

Ya koma taka leda a Roma a 2024, wanda kawo yanzu ya yi wa fafatawa 18 a kungiyar da ke buga babbar gasar tamaula ta Italiya, wato Serie A.